Abin da Shugaban UBEC, Mahmood Mohammed, yake fadawa ‘Yan uwansa a wayar tarho

Abin da Shugaban UBEC, Mahmood Mohammed, yake fadawa ‘Yan uwansa a wayar tarho

A halin yanzu dai a Najeriya, Masu garkuwa da mutane su na cigaba da cin karensu babu babbaka, musamman a kan hanyar Kaduna zuwa Garin Abuja, duk da irin kokarin da rundunar jami’an tsaro ke yi.

Mun samu wani sautin murya a yau 30 ga Watan Afrilun nan inda aka ji Alhaji Mohammed Mahmood, wanda shi ne shugaban hukumar UBEC na kasa, yana waya da Iyalinsa domin a ceto rayuwarsa, jim kadan bayan an yi sace shi.

Iyalan Shugaban na UBEC sun yi kokarin hada Naira Miliyan 13 a cikin kankanin lokaci kamar yadda mu ka ji su na fada a waya. An ji Mohammed Mahmood, yana cewa lokaci yana kurewa don haka ayi maza a hada kudi a ceto sa.

Mohammed Mahmood ya fadawa wani mutumi ta wayar salula cewa su yi maza su tattara kudin da ake bukata domin a sake su cikin sa’a guda. Wanda su ke wayar ya kuma bayyana masa cewa an tara fiye da Miliyan 13 tun a cikin dare.

KU KARANTA: Garkuwa da mutane: An biya Miliyan 60 kafin a saki Shugaban UBEC

Abin da Shugaban UBEC, Mahmood Mohammed, yake fadawa ‘Yan uwansa a wayar tarho

An bukaci Miliyoyi domin fansa bayan sace Shugaban UBEC a hanyar Abuja
Source: UGC

Shugaban na UNEC ya koka da cewa su na fama da karancin Naira, domin kuwa da ace wadanda su ka tsare sa su na bukatar Daloli, da tuni sun bada domin su tsira da lafiyarsu. A cikin wayar, Mahmood yana cewa ana kula da lafiyarsu.

A karshen wayar, Alhaji Mohammed Mahmood ya fadawa ‘Yan uwan na sa cewa su tattara kudin da su ka hada su mikawa wani Bawan Allah mai suna Husaini wanda yake Hamdala domin ya kawo kudin da za a kubutar da shi washegari.

Idan ba ku manta ba, an sace Mohammed Mahmood da kuma ‘Diyarsa bayan an harbe Direbansa. Kawo yanzu mun samu labari cewa an sake su da safiyar yau bayan sun biya makudan miliyoyin kudi.

Domin sauraron wannan sauti sai a biyo wannan shafi na Jaridar Daily Trust

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel