Dogara ya bukaci a kama shugaban hukumar RMAFC

Dogara ya bukaci a kama shugaban hukumar RMAFC

Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya amince da aika sammaci ga shugaban hukumar raba kudaden shiga da gwamnati ta samu (RMAFC), Shettima Umar-Gana saboda saba wa sashe na 4 na dokar majalisa da ke magana a kan iko da karfin da majalisa keda shi.

Shugaban kwamitin bincike a kan bayanan da hukumar RMAFC ke sarrafa wa, Mark Gbillah, ne ya sanar da hakan yayin zaman jin ra'ayin jama'a da kwamitin ya yi ranar Talata a Abuja.

Gbillah ya ce yin hakan ya zamo wajibi ne biyo bayan kin mututunta bukatar majalisa na bayar da bayana ga kwamitinsa duk da hakan bai saba da kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Ya ce Umar-Gana ya saba wa sashe na 4 na iko da karfin da majalisa keda shi.

Kazalika ya yi alla-wadai da umarnin Gana ya bayar ga ragowar ma'aikatu da hukumomin gwamnati na kin bawa kwamitin bincike na majalisar wakilai bayanan da zai taimake su a aikin da suke yi.

Dogara ya bukaci a kama shugaban hukumar RMAFC

Yakubu Dogara
Source: Depositphotos

Dan majalisar ya kara da cewa babu abinda zai hana majalisar gudanar da aikinta na kare hakkin 'yan Najeriya bisa gwadaben gaskiya, rikon amana da adalci kamar yadda doka ta shimfida a sashe na 88 da 89 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

DUBA WANNAN: Ka gaggauta dawo da N14.3b da ka karkatar - Majalisa ta umarci ministan Buhari

Hukumar RMAFC ce ke fitar da taswirar rabon kudaden shiga da gwamnati ta samu a tsakanin hukumomi gwamnati da kuma fitar da taswirar tsarin biyan albashin ma'aikata a dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Majalisar wakilai na neman bayanai a kan manhajar da hukumar RMAFC ke amfani da ita wajen bawa hukumomi kason kudi da kuma kayyade albashin ma'aikata, domin yin gyara ko kwaskwarimar da zai tabbatar dukkan ma'aikata sun samu karin albashin da gwamnatin tarayya tayi a cikin watan nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel