Hukumar DPR ta nemi a koyawa direbobin tanka dubarun kashe wuta

Hukumar DPR ta nemi a koyawa direbobin tanka dubarun kashe wuta

- Hukumar DPR tace akwai bukatar direbobin tanka su koyi kashe gobara

- Koyon kashe gobarar zaiyi matukar taimakawa domin ceto rayuka dama dukiyoyi

A bisa yinkurin magance matsalar gobarar motocin dake dakon man fetur, hukumar DPR ta roki jagororin hukumar NUPENG da ta baiwa direbobinta horo akan kashe gobara domin shawo kan matsalar konewar tankoki.

Shagaban kungiyar reshen jihar Gombe, Alhaji Abdullahi Abawa shine ya bada wannan shawara ranar Talata a Gombe, daidai lokacin da yake tsokaci akan al’amarin da ya auku a garin Gombe ranar 13 da 17 ga watan Afrilu wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da yawa yayinda saura suka samu rauni.

Hukumar DPR ta nemi a koyawa direbobin tanka dubarun kashe wuta

Hukumar DPR ta nemi a koyawa direbobin tanka dubarun kashe wuta
Source: Depositphotos

Abawa yayi korafi akan gazawar gwamnatin jiha da kuma ta tarayya akan wanna lamari. Inda ya nuna cewa babu wadatattun kayan kashe wuta.

KU KARANTA:Yanzun nan: shugaban hukumar ilimi ta UBEC da ‘yar shi sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane

Ya kara da cewa idan aka koyawa direbobin yadda zasu kashe gobarar zai tamaka kwarai da gaske musamman wurin ceto rayuka da kuma dukiyoyi.

Ita kuwa hukumar DPR, ta sake shawartar kungiyar kasuwancin man fetur mai zaman kanta ta kasa wato IPMAN na su hada hannu da NNPC domin samar da sashen kashe a gobara irin wannan na koda ta kwana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel