An bayyana miliyoyin nairorin da iyalan shugaban UBEC suka biya kafin ya fito daga hannun masu garkuwa

An bayyana miliyoyin nairorin da iyalan shugaban UBEC suka biya kafin ya fito daga hannun masu garkuwa

Wani rahoto na baya bayan nan ya tabbatar da cewa sai da iyalan shugaban hukumar ilimi ta bai daya UBEC, Alhaji Muhammad Mahmood suka hada makudan kudade da suka kai naira miliyan sittin (N60,000,000) da suka biya yan bindigan da suka yi garkuwa dashi da diyarsa kafin suka sakosu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan bayani ya fallasu ne daga wani rikodin na hirar wayar tarho da aka yi tsakanin Muhammad da wani dan uwansa mai suna Saleh a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu jim kadan bayan an daukeshi.

KU KARANTA: Goje ya dau alwashin kin janyewa daga neman shugabancin majalisa har sai Buhari ya lallashe shi

An bayyana miliyoyin nairorin da iyalan shugaban UBEC suka biya kafin ya fito daga hannun masu garkuwa
Muhammad a Yasmin
Source: Twitter

A daidai kauyen Katari dake kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ne gungun yan bindiga sanye da kayan Sojoji suka tare motar Muhammad, suka yi awon gaba dashi da diyarsa Yasmin bayan sun kashe direbansa, sai dai da tsakar ranar Talata suka sakosu duka bayan biyan makudan kudin fansa.

An jiyo Muhammad a cikin wannan rikodin yana magiya ga iyalansa dasu gaggauta wajen tattara kudin da za’a a biya don fansarsu saboda babu lokaci. “Saleh don Allah ku gaggauta, babu lokaci, kuma sai an dauki lokaci kafin mu cimma inda za’a mika musu kudin, cikin awa daya suke son kudin.” Inji shi.

Yayin da shi kuma Saleh ya amsa masa da cewa “A yanzu haka aikin da muke tayi kenan, mun samu naira miliyan goma sha uku, matsalar da muke fuskanta a yanzu shine dare yayi, amma akwai wanda yace zai bamu cikon naira miliyan 50 idan gari ya waye, idan kuma dala suke so, zamu iya basu a daren nan.”

Sai shima Muhammad ya amsa masa da cewa “Na gane, amma idan za’a samu kudin, kaje ka amsosu a duk inda suke, bamu son mu wuce awa daya a hannun mutanen nan, kaga yanzu akwai miliyan 30 a kasa, ga miliyan 13 an samu, munada miliyan 43 kenan, muna neman saura miliyan 17 kenan.

“Kaga mutanen nan suna bamu kyakkyawar kulawa, Yasmin ta samu rauni a kafarta, amma suna taimaka mata, ka nemo kudin a duk inda zaka samoshi.” Inji shi.

Daga karshe Saleh ya tabbatar masa cewa zasu yi iya kokarinsu don samu kudaden da yan bindigan suke nema, inda shima Muhammad yace a mika kudaden zuwa ga wani Malam Hussaini dake Hamdala Hotel wanda zai kai kudaden.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel