‘Yan bingida sunyi awon gaba da mataimakin rajistaran jami’ar jihar Taraba

‘Yan bingida sunyi awon gaba da mataimakin rajistaran jami’ar jihar Taraba

-An sace mataimakin rajistaran jami'ar jihar Taraba

-Tirkashi, an sace mataimakin rajistaran jami'ar jihar Taraba har gida

A safiyar ranar Talata ne yan bindiga sukayi awon gaba da Malam Sanusi Sa’ad, mataimakin rajistaran Jamiar Jihar Taraba dake Jalingo.

Dakta Samuel Shikaa, shugaban hukumar malaman jami’a wato (ASUU), reshen jihar Taraba ya tabbatar da faruwar wannan mummunan al’amari ga ma nema labarai.

‘Yan bingida sunyi awon gaba da mataimakin rajistaran jami’ar jihar Taraba

‘Yan bingida sunyi awon gaba da mataimakin rajistaran jami’ar jihar Taraba
Source: Twitter

KU KARANTA:An rufe wata mata saboda laifin satar naira 297,000

Shikaa yace Malam Sa’ad wanda shine mai kula da sashen yada labarai na jami’ar an sace shine a gidansa dake jerin gidajen ma’aikatan jami’ar da misalin karfe dayan dare.

Ya kara da cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka shigo ta bayan jami’ar wurin da ba’a katange ba suka dauke rajistaran zuwa wani wuri da bamu sani ba.

Alhaji Sa’ad Khalid dan uwan wanda aka sace, ya shaidawa manema labarai cewa an kirashi a waya inda aka nemi ya bada kudin fansa.

Sai dai bai bayyana ko nawa ‘yan ta’addan suka nema ba amma yace suna kan yin ciniki domin haka har yanzu basu samu matsaya ba.

Haka zalika, kwamishinan yan sandan jihar Taraba ya gargadi masu aikata irin wadannan laifuka da su yi gaggawar barin garin na Taraba domin idan har suka shigo hannu baza suji da dadi ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel