NAHCON ta yaba ma NDLEA kan gano yadda ake yiwa matafiya bita da kullin kwaya a kayansu

NAHCON ta yaba ma NDLEA kan gano yadda ake yiwa matafiya bita da kullin kwaya a kayansu

Hukumar da ke kula da zirga-zirgan alhazai na Najeriya (NAHCON) ta yaba ma hukumar hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) akan yadda suka gano hanyar da wadansu miyagun mutanee ke sanya wa matafiya da basu ji ba basu gani ba miyagun kwayyi a jakunkunansu.

Kakakin hukumar NAHCON, Hajiya Fatima Usara c eta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.

Usara ta bayyana cewa ayyukan wadannan miyagun mutane ya sanya rayuwar matafiya wadanda ba su jiba ba su gani ba cikin wani mawuyacin yanayi.

Ta bayar da tabbacin cewa NAHCON da NDLEA za su ci gaba da aiki tare domin tabbatar da maniyyata aikin hajji da umara sun je ayyukansu lafiya sun dawo lafiya.

NAHCON ta yaba ma NDLEA kan gao yadda ake yiwa matafiya bita da kullin kwaya a kayansu

NAHCON ta yaba ma NDLEA kan gao yadda ake yiwa matafiya bita da kullin kwaya a kayansu
Source: UGC

Ta nusar da cewa hukumar NAHCON din da NDLEA za su yi amfani da dukkanin hanyoyin da suka samu ta hanyar amfani da kimiyya a cibiyoyin kwashe kayayyakin na tasoshin jiragen sama a dukkanin kasarnan domin tabbatar da tsaron mahajjaci da kayansa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2019, ta kara ta da wajen N86bn

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hukumomin kasar Saudiyya sun saki Zainab Aliyu, matashiyar nan 'yan Najeriya da aka kama bisa zarginta da shiga da kwaya kasar saudiyya.

A jawabin da babban sakatare a ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ya fitar, ya ce yanzu haka Zainab na ofishin jakadancin Najeriya dake kasar Saudiyya.

Kazalika, ya bayyana cewa hukumomin kasar Saudiyya za su saki Ibrahim Abubakar, wani dan Najeriya da ya samu irin matsalar Zainab a kasar Saudiyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel