Buhari yana yabawa jajircewa da kwazo bisa aiki - Omoboriowo

Buhari yana yabawa jajircewa da kwazo bisa aiki - Omoboriowo

Mista Bayo Omoboriowo, babban hadimin mai daukan hoto na shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata ya yi arin haske dangane da kyawawan dabi'u masu sanya farin ciki da annashuwa ta gamsuwa a zuciyar uban gidan sa.

Kwararren mai daukan hoton ya bayyana cewa, shugaban kasa Buhari ya kasance mutum mai matsananciyar bukata ta yabawa jajircewa, gwagwarmaya da kuma kwazo wajen gudanar da aiki tukuru cikin inganci da nagarta.

Buhari yana yabawa jajircewa da kwazo bisa aiki - Omoboriowo
Buhari yana yabawa jajircewa da kwazo bisa aiki - Omoboriowo
Source: Facebook

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Mista Bayo ya yi furucin hakan a yayin halartar taron karawa juna sani a kan sana'ar daukar hoto na shekarar 2019 da aka gudanar cikin dakin taro na Landmark da ke birnin Victoria Island a jihar Legas.

Rahotanni kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, kamfanin sadarwa na YD Agency shi ne ya dauki nauyin taron wanda aka gudanar da babbar manufa ta inganta harkokin sana'ar daukan hoto a Najeriya.

KARANTA KUMA: Karuwanci: Kotun Abuja ta yankewa Mata 27 hukuncin dauri na wata guda

Kazalika an gudanar da taron na karawa juna sani da manufa ta kawo karshe tare da warware matsalolin da masu sana'ar daukan hoto ke fuskanta a fagen sana'o'in su cikin Najeriya.

Mista Bayo yayin fashin baki a kan tarayyar sa da uban gidan sa ya bayyana cewa, shugaba Buhari ya kasance mutum mai yabawa gwagwarmaya ta kwazon aiki da jajircewa da suka sanya ya zamto madubin dubawa a idon duniya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel