Ramadan: Malamai sun gargadi yan kasuwa game da tsawwala farashin kayan masarufi

Ramadan: Malamai sun gargadi yan kasuwa game da tsawwala farashin kayan masarufi

Babban limamin Masallacin Ore Oluwa dake garin Ilorin na jahar Kwara, Alhaji Isiaka Usman yayi kira ga yan kasuwa dake fadin Najeriya dasu kaurace ma tsawwala farashin kayayyakin masarufi don samun kazamar riba, musamman a watan azumin Ramadana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Usman yayi wannan kira ne a ranar Talata a garin Ilorin inda ya bayyana halayyar wasu yan kasuwa dake sayar da kayansu da tsada a watan Ramadana a matsayin mugunta da rashin Imani.

KU KARANTA: Masarautar Machina ta nada gwamnan jahar Yobe wani muhimmin sarauta

“Yan kasuwa suna amfani da damar watan Ramadana wajen kara farashin kayansu fiye da kima don su kuntata ma Musulmai, sun mayar da Ramadan watan samun kazamar riba, suna sane da cewa Musulmai na azumi, don haka dole su nemi sayan kayan abinci da kayan marmari.

“Wannan matsala ta zama ruwan dare tsakanin yan kasuwanmu, tamkar mutum yana nema ma kansa fushin Allah ne saboda babu yadda jama’a zasu yi idan basu saya ba, shi yasa nake kira ga yan kasuwa da suji tsoron Allah su kauce ma wannan mummunar dabi’a.” Inji shi.

Da yake yau Talata 30 ga watan Afrilu yayi daidai da 24 ga watan Sha’aban, don haka ana sa ran fara Azumin watan Ramadana nan da kwanaki 6 ko 5, ya danganta da kwanakin da watan Sha’aban yayi, amma sai an samu sanarwa daga fadar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel