-Muhammad Mahmood da 'yar shi sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane
-Shugaban hukumar ilimi ta bai daya ya samu kubuta tare da yar shi ba tare da an biya kudi ba
Bayan awa 24 da sace shugaban hukumar ilimi ta bai daya tare da ‘yar shi sun samu yanci kuma sun koma gida a ranar Talata.
Hadiminsa ne ya tabbatar da cewa lallai an saki maigidan nashi ta hanyar wayar tarho da yayi da manema labara a Abuja ranar Talata. Ya sake cewa maigidan nashi da ‘yar shi an sako su da misalign karfe daya da minti talatin na ranar Talata.

Yanzun nan: shugaban hukumar ilimi ta UBEC da ‘yar shi sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane
Source: UGC
KU KARANTA:An rufe wata mata saboda laifin satar naira 297,000
Bugu da kari, ya sanar da manema labarai cewa ba biya kudin fansa fa kafin maigidan nashi da ‘yar sa su fito daga hannun wadanda suka sace su.
Muhammad Mahmood wanda shine shugaban hukumar ilimi ta bai dayan an sace shi ne tare da diyar shi a hanyar zuwa Abuja daga Kaduna.
A yayin hakan ma direbansa aka harbeshi har lahira. Wannan abu dai ya auku ne a daidai kauyen Katari wanda ke Zuba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa