Majalisar dattijai ta bukaci ministan Buhari ya dawo da biliyan N14.3 da ya karkatar

Majalisar dattijai ta bukaci ministan Buhari ya dawo da biliyan N14.3 da ya karkatar

Majalisar dattijai ta umarci ministan kamafanoni da masana'antu, Dakta Okechukwu Enelamah, da babban darektan hukumar tsara fitar da kaya zuwa kasashen ketare (NEPZA), Terhemba Nongo, da su gaggauta dawo da zunzurutun kudi da yawansu ya kai biliyan N14.3 zuwa asusun gwamnatin tarayya.

A umarnin da majalisar ta bawa shugabannin biyu a ranar Litinin, ta bukaci su gaggauta dawo da kudin da suka karkatar da su daga kudaden da aka ware wa hukumar NEPZA a cikin kasafin kudin shekarar 2017.

A cikin takardar da shugaban kwamitin kamfanoni da masana'antu na majalisar dattijai, Sabo Nakudu, ya sa hannu a kanta, majalisar ta gargadi ministan da darektan NEPZA da ko dai su gaggauta bin umarnin majalisar ko kuma su fuskanci fushin ta.

Kwamitin majalisar ya yi zargin cewar an gaggauta karkatar da N14.3b daga asusun NEPZA zuwa wani kamfani mai zaman kansa a ranar 8 ga watan Afrilu duk da kasancewar majalisar ta ja hankalin ministan da darektan a kan yunkurin karkatar da kudin.

Majalisar dattijai ta bukaci ministan Buhari ya dawo da biliyan N14.3 da ya karkatar

Okechukwu Enelamah
Source: Depositphotos

Nakudu ya ce, da farko kudin na ajiye ne a cikin asusun hukumar NEPZA dake babban bankin kasa tun bayan ware su a kasafin kudi na shekarar 2017, kafin daga bisani a fitar da su zuwa asusun wani kamfani mai zaman kansa, kimanin sati biyu da suka wuce.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Hukumar Saudiyya ta saki Zainab Ali, za a saki Ibrahim Abubakar gobe

Da yake magana da manema labarai ranar Litinin, Nakudu ya ce; "domin dakile wannan almundahana, kwamitin da nake jagoranta ya rubuta takarda zuwa ga gwamnan babban bankin kasa a ranar 8 ga watan Afrilu a kan kar ya saki kudin, amma bayan ya samu wasikar sai ya sanar da mu cewar tuni hukumar NEPZA ta fitar da kudin zuwa asusun wani kamfani bisa umarnin minista."

"Ba zamu yarda da wannan abu ba, a saboda haka dole a dawo da kudin cikin asusun gwamnatin tarayya nan da sati daya ko kuma mu dauki mataki."

Sai dai, hukumar NEPZA ta kafe a kan cewar ta fitar da kudin ne bisa ka'ida da kuma tsarin gwamnati na son bunkasa harkokin masana'antu da saka hannu jari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel