Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2019, ta kara ta da wajen N86bn

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2019, ta kara ta da wajen N86bn

- Majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2019

- Ta gabatar da naira tiriliyan 8.916 a matsayin kasafin kudin 2019 sabanin naira tiriliyan 8.83 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata

- Adadin ya dara abunda Buhari ya gabatar a taron majalisun na kasa a ranar 19 Disamba da naira biliyan 86

Majalisar dattawa ta amince da naira tiriliyan 8.916 a matsayin kasafin kudin shekarar 2019 sabanin naira tiriliyan 8.83 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukata.

An amince da sabon kasafin kudin ne bayan Danjuma Goje, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kudi, ya gabatar da rahoto a majalisan a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2019, ta kara ta da wajen N86bn

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta gabatar da kasafin kudin 2019, ta kara ta da wajen N86bn
Source: UGC

Adadin ya dara abunda Buhari ya gabatar a taron majalisun na kasa a ranar 19 Disamba da naira biliyan 86.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ne ya bayyana hakan, inda ya nuna godiyarsa gay an majalisa da suka cika wa’adin da aka diba domin gabatar da dokar.

Legit.ng ta kawo Saraki na fadin: “Ina fatan cewa da wannan kasafin kudin da aka gabatar, ina fatan bangaren zartarwa za ta tabbatar da cikakken aikin kasafin domin amfanin yan Najeriya baki daya.

“Ina mika godiya ga abokan aikinmu, musamman akan fahimtarsu da kuma wadanda suka daidaici ranar yau da aka bayar domin gabatar da sakafin sannan ina godiya ga kwamitin kasafin kudi ma.”

Sun kuma amince da naira biliyan 10 na tallafi ga Zamfara biyo bayan ayyukan yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ya addabi mutanen jihar.

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a sake shiga cikin matsananci matsi na tattalin arziki a Najeriya a sabuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KAARANTA KUMA: Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, gwamna Yari da ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya ce Najeriya za ta fuskanci wani sabon matsi na tattalin arziki a tsakiyar shekarar 2020.

Baya ga haka gwamna Yari yayin karin haske dangane da yadda gwamnonin Najeriya suka yiwa kawunan su karatun ta nutsu tare da fahimtar cewa ciyo bashi ba zai taba kubutar da kasar nan ba daga kalubalai na tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel