Yanzu Yanzu: Boko Haram sun kai farmaki kauyen Adamawa, sun kashe mutum 26, sun raunata wasu da dama

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun kai farmaki kauyen Adamawa, sun kashe mutum 26, sun raunata wasu da dama

Akalla mutane 26 ne suka mutu sannan da dama sun jikkata a wani mumunan hari da yan ta’addan Boko Haram suka kai yankin Madagali da ke jihar Adamawa a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu.

Mazauna yankin sunce yan bindigan Boko Haram sun zo da dama a kan Babura inda suka shiga kauyen Kudakaya a Madagali da misalin karfe 7:00 na yamma.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Othman Abubakar, ya tabbatar da harin.

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun kai farmaki kauyen Adamawa, sun kashe mutum 26, sun raunata wasu da dama

Yanzu Yanzu: Boko Haram sun kai farmaki kauyen Adamawa, sun kashe mutum 26, sun raunata wasu da dama
Source: Twitter

“An sanar dani cewa yan ta’addan Boko Haram sun kai hari kauyen. Ban san adadin mutanen da suka mutu ba, amma an tura jami’an tsaro domin su kwantar da lamarin.”

Wannan na daya daga cikin hare-haren da yankin ta fuskanta a baya-bayan nan.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kimanin rayukan dakarun sojojin Najeriya biyar sun salwanta yayin da aka nemi sojoji 30 aka rasa biyo bayan wani mummunan hari da kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ta kai kan wani sansanin dakaru da ke jihar Borno.

KU KARANTA KUMA: Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, mayakan boko haram tare da hadin gwiwar kungiyar ta'adda ta ISIS, sun yiwa dakarun sojin Najeriya diban karan mahaukaciya a ranar Juma'ar cikin jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel