Kungiyar Izala ta gabatar da muhimmin bukata a gaban gwamnati

Kungiyar Izala ta gabatar da muhimmin bukata a gaban gwamnati

- Kungiyar Izala ta bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su karfafa kokarinsu wajen ganin sun samar da isasshen wutar lantarki a fadin kasar

- Ta kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su mayar da hankali wajen samar da wutan lantarki a yankunan karkaran da ke kasar don inganta samar da ayyuka ga al’umma tare da inganta tattalin arzikin kasar

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su karfafa kokarinsu wajen ganin sun samar da isasshen wutar lantarki a fadin kasar.

Kungiyar ta cigaba da yin kira ga gwamnati a dukkan matakai da su mayar da hankali wajen samar da wutan lantarki a yankunan karkaran da ke kasar don inganta samar da ayyuka ga al’umma tare da inganta tattalin arzikin kasar.

Kungiyar ta bayyana kiran ne a taro na kasa na mako 26 na shekara shekara da kungiyan ta gudanar a Jos a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu.

Kungiyar Izala ta gabatar da muhimmin bukata a gaban gwamnati

Kungiyar Izala ta gabatar da muhimmin bukata a gaban gwamnati
Source: Facebook

Sakon na dauke da sa hannun babban mai gudanarwa na kungiyar na kasa a taro da gasar alkur’ani, Hafiz Aminu Yusuf.

KU KARANTA KUMA: Hukumar aikin Hajji na Najeriya ta dauki lauyoyin Saudiyya da za su ceto Zainab Aliyu daga gidan yari

Har ila yau ya bukaci hukumomin tsaro dasu karfafa ayyuka wajen kau da laifuffuka a kasan don guje ma batanci ga martabar kasan.

Kumgiyar ta kuma roki gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da su tabbatar an cimma buri, adalci da gaskiya wajen nadin alkalai a kotun Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa '

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel