Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Wasu dandazon dalibai matasa sun gudanar da zanga-zanga neman a sakin 'yar Najeriyar nan, Zainab Aliyu wacce ke tsare a kasar Saudiyya.

Daliban sun gudanar da zanga-zangar ne a ranar Talata, 29 ga watan Afrilu a jihar Kano, inda masu zanga-zangar suka nemi a sake ta ba tare da wani ba ta lokaci ba.

An fara zanga-zangar ne daga Jami'ar tuna wa da Yusuf Maitama Sule a Kofar Nasarawa.

Jami'an tsaron Saudiyya sun kama Zainab Aliyu ne jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara ita da mahaifiyarta Maryam da kuma 'yar uwarta Hajara.

Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Dalibai sun gudanar da zanga-zanga neman a sakin 'yar Najeriyar nan, Zainab Aliyu wacce ke tsare a kasar Saudiyya
Source: UGC

Sun zarge ta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta.

Amma tuni hukumar yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewa wasu ma'aikata ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) suka saka mata kwayar a jakarta.

Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Hukumar Saudiyya ta zargeta da safarar kwayar Tramadol har guda 2,000 bayan da aka ga kwayoyin a wata jaka mai dauke da sunanta
Source: UGC

Uku daga cikinsu ma'aikata ne da ke tantance kayayyakin matafiya, daya ma'aikacin wani kamfanin sufurin jirgin sama ne, sauran biyun kuma jmai'an tsaro ne a filin jirgin saman.

Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano

Dandazon jama’a sun fito zanga-zanga kan batun Zainab Aliyu a Kano
Source: UGC

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Hukumar aikin Hajji na Najeriya (NAHCON), ta sanar da daukar lauyoyin Saudiyya domin su taimaka wajen sakin yar Najeriya, Zainab Aliyu wacce aka zarga da safarar miyagun kwayoyi bisa kuskure.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Fasinjoji 4 sun mutu yayinda jirgin kasa ya kara da adaidaita sahu a Lagas

Yunkurin NAHCON na daga cikin kokarin da Najeriya ke yi a masarautar, yayinda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci babban alkalin kasar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya sanya baki a lamarin.

Hukumar a wata sanarwa daga kakakinta, Fatima Usara, ta bayyana cewa ana neeman ceto Zainab wacce aka dasa wa miyagun kwayoyi a Jakarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel