An rufe wata mata saboda laifin satar naira 297,000

An rufe wata mata saboda laifin satar naira 297,000

-An kai wata mata gaban kotun a dalilin satar N297,000 a Badagry dake Legas

-Bayan da alkali ya saurari shari'ar ya amince da bada belin wannan mata

‘Yan sanda sun gurfanar da wata mata mai suna Deborah Adeoba ‘yar shekara 24 da haihuwa a gaban kotun Majistiri dake Badagry ranar Talata bisa zargin satar naira 297,000.

Wacce ake tuhumar da aka sakaya adireshinta dai ana tuhumar tane akan shiga ba tare da izini ba da kuma laifin laifin sata wanda taki amincewa ta aikata.

An rufe wata mata saboda laifin satar naira 297,000
An rufe wata mata saboda laifin satar naira 297,000
Source: Facebook

KU KARANTA:Dalilin da yasa bazan bar APC ba, inji gwamnan Kogi

Wanda ya shigar da wannan kara wato Sajan Ayodele Adeosun ya shaidawa kotu cewa tabbas wacce ake zargin ta aikata wannan laifin ne a watan Fabrairu da misalin karfe daya na dare a unguwar Ilogbo dake Legas.

Adeosun ya kara da cewa, ita dai wannan matar ta balle ofishin Kingsley Uba inda ake ajiyar kudi ta hanyar amfani da wani makulli na daban.

“ Wacce ake tuhumar ta sace naira 297,000 da wasu kayayyakin mai ofishin, yayinda mai ofishin ne ya damketa da kanshi a daidai lokacin da take satar. Kana kuma baiyi wata wata ba ya mikata hannun hukumar ‘yan sanda.” Adeosun ya labartawa kotun.

Mai shari’ar wannan kotun, Patrick Adekomaya ya aminta da cewa wacce ake tuhumar zata iya samun beli akan kudi naira 100,000. Sannan kuma daga karshe ya dage sauraron karar zuwa 28 ga want Mayu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel