A shirye nake na fuskanci shari’a koda a kan mulki ne – Zababben gwamnan Bauchi

A shirye nake na fuskanci shari’a koda a kan mulki ne – Zababben gwamnan Bauchi

- Zababben gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed yace bai yi kowani laifi ba sannan kuma shi a shirye yake ya fuskanci shari’a

- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ce dai ta gurfanar dashi kan kin kaddamar da ainahin kadarorinsa da ba EFCC bayanan karya

- Bala yace duk wannan kullin wasu mutane ne da ke adawa dashi

Bala Mohammed, zababben gwamnan jihar Bauchi, yace bai yi kowani laifi ba sannan kuma shi a shirye yake ya fuskanci shari’a.

Mohammed ya bayyana hakan a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu yayinda yake zantawa da manema labarai bayan hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar dashi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta sanya sabbin tuhume-tuhume akan sa kan kin kaddamar da ainahin kadarorinsa da ba EFCC bayanan karya.

A shirye nake na fuskanci shari’a koda a kan mulki ne – Zababben gwamnan Bauchi

A shirye nake na fuskanci shari’a koda a kan mulki ne – Zababben gwamnan Bauchi
Source: UGC

Halilu Yusuf, alkalin da ke jagorantar shari’an bai hallara ba a yayinda ya kamata ayi zaman kotu a jiya Litinin.

KU KARANTA KUMA: Hukumar aikin Hajji na Najeriya ta dauki lauyoyin Saudiyya da za su ceto Zainab Aliyu daga gidan yari

Ana kuma zargin Mohammed da amsar cin hancin naira biliyan 1.6 na kasa yayinda yake rike da mukamin ministan babbar birnin tarayya, Abuja.

Sai dai zababben gwamnan yace duk wannan kullin wasu mutane ne da ke son gabatar da lamarin a matsayin sabo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel