Dole gwamnati ta zage dantse wajen kawar da kalubalan da ake fuskanta a Najeriya - Sultan

Dole gwamnati ta zage dantse wajen kawar da kalubalan da ake fuskanta a Najeriya - Sultan

- Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad na uku, ya bayyana damuwar sa kan yadda rashin tsaro da matsin rayuwa suka zamto katutu a kasar nan

- Sultan na Sakkwato ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da wani uzuri na rashin kawo karshen kalubalai da aka fuskanta cikin kasar

Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa'ad na uku, ya bayyana mafi girman damuwa kan yadda rashin tsaro, katutu na talauci da kuma sauran ababe na kuncin rayuwa su ka yiwa kasar nan sarkakiya tare da kasancewar su karangiya a cikin ta.

Dole gwamnati ta zage dantse wajen kawar da kalubalan da ake fuskanta a Najeriya - Sultan

Dole gwamnati ta zage dantse wajen kawar da kalubalan da ake fuskanta a Najeriya - Sultan
Source: Twitter

Sultan na Sakkwato wanda ya kasance babban jagora na cibiyar koli mai kula da al'amurran da suka shafi addinin Islama, ya ce akwai babbar damuwa dangane da yadda aka gaza warware matsalolin da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa, Sultan na Sakkwato ya bayyana hakan ne yayin taron shekara na kungiyar Jama'atu Nasril Islam kamar yadda aka saba domin yiwa watan Azumin Ramalana lale maraba da aka gudanar a ranar Litinin cikin garin Kaduna.

Sarkin Musulmi ya ke cewa, duk da arzikin jagorori na gari da kuma macancanta, Najeriya ba ta da wani uzuri na gazawar ta a kan rashin warware matsaloli da al'ummar kasar ke fuskanta a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Za mu kara adadin ma'aikatan hukumomin tsaro a Najeriya - Buhari

Ya yi kira ga daukacin al'ummar Najeriya mabiya addinin Islama, da su yi riko da kyakkyawan tafarki da koyarwar mafi girman Littafai watau Al-Qur'ani da ya kasance kundi kuma ginshiki na madogarar rayuwa musamman a lokutan watan Azumi da ya karato.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel