Hukumar aikin Hajji na Najeriya ta dauki lauyoyin Saudiyya da za su ceto Zainab Aliyu daga gidan yari

Hukumar aikin Hajji na Najeriya ta dauki lauyoyin Saudiyya da za su ceto Zainab Aliyu daga gidan yari

- Hukumar aikin Hajji na Najeriya, ta sanar da daukar lauyoyin Saudiyya domin su taimaka wajen sakin yar Najeriya, Zainab Aliyu

- Zainab dai na tsare a kasar Saudiyya bayan an kamata bisa kuskure kan zargin safarar miyagun kwayoyi

- Haka zalika Muhammadu Buhari ya umurci babban alkalin kasar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya sanya baki a lamarin

Hukumar aikin Hajji na Najeriya (NAHCON), ta sanar da daukar lauyoyin Saudiyya domin su taimaka wajen sakin yar Najeriya, Zainab Aliyum wacce aka zarga da safarar miyagun kwayoyi bisa kuskure.

Yunkurin NAHCON na daga cikin kokarin da Najeriya ke yi a masarautar, yayinda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci babban alkalin kasar kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, da ya sanya baki a lamarin.

Hukumar a wata sanarwa daga kakakinta, Fatima Usara, ta bayyana cewa ana neeman ceto Zainab wacce aka dasa wa miyagun kwayoyi a Jakarta.

Hukumar aikin Hajji na Najeriya ta yi dauki lauyoyin Saudiyya da za su ceto Zainab Aliyu daga gidan yari

Hukumar aikin Hajji na Najeriya ta yi dauki lauyoyin Saudiyya da za su ceto Zainab Aliyu daga gidan yari
Source: Twitter

Kakakin NAHCON ta bayar da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da aiki da hukumar NDLEA domin tabbatar da kore lamarin miyagun kwayoyi a lokacin Umrah da Hajjin 2019.

KU KARANTA KUMA: Cikin yan siyasa ya duri ruwa yayinda INEC ke bibiyar yadda aka kashe kudin kamfen

Hukumomin kasar Saudiyya ta kama Zainab wacce ta kasance dalibar jami’ar Maitama Sule, Kano, a ranar 26 ga watan Disamban 2018 kan zargin tafiya da jaka mai dauke da kayayyakin da aka aka haramta wato tramadol.

Wacce ake zargin tayi tafiyar ne ta filin jirgin Mallam Aminu Kano, MAKIA, don aikin umurah tare da mahaifiyarta Maryam da kuma yar’uwarta Hajara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel