Ziyarar Buhari bai saba ma doka ba – BMO ga PDP

Ziyarar Buhari bai saba ma doka ba – BMO ga PDP

Kungiyar labaran Buhari (BMO) ta mayar da martani ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) cewa tafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai saba kowace doka ko kundin tsarin mulki ba.

A wani jawabi dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Niyi Akinsiju da kuma sakataren kungiyar Cassidy Madueke, BMO tace Shugaba Buhari shine Shugaban Najeriya na farko da ya tsaya akan kundin tsarin mulkin Najeriya a wannan fannin.

Kungiyar ta shawarci PDP da ta janye daga kai hare-haren ba gaira ba dalili a kafofin watsa labarai kan ziyarar kai da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai kasar Birtaniya kwanan nan.

Ziyarar Buhari bai saba ma doka ba – BMO ga PDP

Ziyarar Buhari bai saba ma doka ba – BMO ga PDP
Source: Depositphotos

Kungiyar Buharin tayi martaninta ne a wani jawabi manema labarai zuwa ga Mistya Uche Secondus, Shugaban jam’iyyar PDDP na kasa inda jam’iyyar ta caccaki ziyarar sa kai da Buhari ya kai Birtaniya kwanan nan ba tare da ya sanar da majalisar dokokin kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Jigawa ta sha alwashin biyan N30,000 mafi karancin albashi

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa wasu kungiyoyi da ake da su masu rajin kare mutunci da martabar damakuradiyya a Najeriya, sun fito sun musanta batun cewa akwai shirin da Bola Tinubu yake yi na ganin an tsige shugaban kasa.

Kungiyar Citizens Watch Nigeria (CWN) da kuma wata mai suna Coalition of Civil Societies and Media Executives for Good Governance in Nigeria wanda aka fi sani da COCMEGG, sun ce babu wani shiri da ake yi na sauke shugaba Buhari.

Wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa babban jigon jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu yana da wani boyayyen nufi na tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan karagar mulki sam ba gaskiya bane.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel