Aikin sojoji na haifar da ýaýa masu idanu – Inji Buhari

Aikin sojoji na haifar da ýaýa masu idanu – Inji Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa ayyukan sojoji akan yan ta’adda na haifar da kyawawan sakamakon da ake burin samu

- Buhari yace kokarin da rundunar sojin ke yi cikin shekaru hudu da suka gabata, ya dawo da martaba da mutuncin Najeriya a tsakanin sauran kasashe

- Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar ya yaba ma Shugaban kasa akan goyon bayan da ya ba rundunar tsawon shekaru hudu da suka gabata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a jiya Litinin, 29 ga watan Afrilu ya bayyana cewa ayyukan sojoji akan yan ta’adda na haifar da kyawawan sakamakon da ake burin samu.

A cewar Shugaban kasar, kokarin da rundunar sojin ke yi cikin shekaru hudu da suka gabata, ya dawo da martaba da mutuncin Najeriya a tsakanin sauran kasashe.

Shugaba Buhari yayi jawabin ne a Eagle Square, Abuja a matsayin bako na musamman a lokacin da rundunar sojin saman Najeriya ke bikin cika shekaru 55.

Aikin sojoji na haifar da ýaýa masu idanu – Inji Buhari

Aikin sojoji na haifar da ýaýa masu idanu – Inji Buhari
Source: Twitter

Da wakilcin mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, runduar sojin sashi na shida sun yiwa Shugaban kasar farati mai kayatarwa.

Wadanda suka halarci taron sun hada da, Shugaban tsaro, Janar Abayomi Olonisakin; babban hafsan soji Laftanal Janar Tukur Buratai; wakilin Shugaban hafsan sojin ruwa da kuma mukaddashin Shugaban yan sandan Najeriya Mohammed Adamu.

KU KARANTA KUMA: Cikin yan siyasa ya duri ruwa yayinda INEC ke bibiyar yadda aka kashe kudin kamfen

Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar ya yaba ma Shugaban kasa akan goyon bayan da ya ba rundunar tsawon shekaru hudu da suka gabata, cewa rundunar sojin sama ta cimma nasarar samar da sabon azure da kuma samar da sabbin rassa da taimakon Shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel