Abin da ya sa na yi fatali da batun hana ‘Yan Majalisa fansho – Dickson

Abin da ya sa na yi fatali da batun hana ‘Yan Majalisa fansho – Dickson

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson, yayi watsi da kudirin da majalisar dokoki ta kawo masa wanda zai bada dama ga ‘yan majalisar jihar su rika samun kudi daga gwamnatin duk wata har su mutu.

Mai girma Seriake Dickson bai amince da kudirin da ‘yan majalisasa su kawo masa gabansa ba, inda yayi watsi da shi duk da cewa majalisar dokokin jihar ta amince da hakan, illa iyaka kurum ana jira ne gwamna ya sa hannu ya zama doka.

A jawabin da mai girma gwamna ya fitar ta bakin Kwamishinansa na yada labarai, Daniel Iworiso-Markson, ya bayyana cewa bai yi na’am da wannan kudiri ba, kuma ya maidawa kakakin majalisar jihar da dalilin daukar wannan mataki.

Gwamnan yake cewa ya gana da ‘yan majalisar jihar Bayelsa a Garinsa na Toru-Orua kafin yayi watsi da wannan kudiri. Seriake Dickson yake cewa tun farko wannan kudiri ya ci karo da sashe na 124 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnoni na kokarin sa baki wajen nada Ministocin Buhari

Abin da ya sa na yi fatali da batun hana ‘Yan Majalisa fansho – Dickson
Gwamna Jihar Bayelsa Dickson ya jefar da kudirin fanshon ‘Yan Majalisa
Source: UGC

Gwamna Dickson yake karin bayani cewa ‘yan majalisar dokoki ba su da damar da za su sa wasu mutane cikin jeringiyar ma’ikatan gwamnati da za a rika biya albashi da kuma fansho. Gwamnan yace bayan haka kuma jihar ba ta da kudi.

Kwamishinan jihar yake cewa duk Najeriya, Bayelsa ce kurum ta nemi ta kawo wannan doka, duk da irin kalubalen da jihar ke fuskanta na samun kudin-shiga da kuma farashin man fetur da yake ta faman wala-wala a kasuwannin Duniya.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa duk da wannan mataki da ya dauka, yana ganin kimar majalisar dokokin jihar irin ya zayyano irin kokarin da yake yi na taimakawa mutanen jihar Bayelsa har kuma yace zai nemi sa hannun sa nan gaba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel