Yanzu Yanzu: Fasinjoji 4 sun mutu yayinda jirgin kasa ya kara da adaidaita sahu a Lagas

Yanzu Yanzu: Fasinjoji 4 sun mutu yayinda jirgin kasa ya kara da adaidaita sahu a Lagas

- Wani mumunan hatsari ya afku tsakanin jirgin kasa da adaidaita sahu a jihar Lagas

- Lamarin yayi sanadiyar mutuwar fasinjoji hudu bayan jirgin kasan ya take adaidaitan

- An tattaro cewa a daidaita sahun mai dauke da fasinjoji ya kafe bayan yunkurin tsallake layin jirgin kasar, wanda hakan yayi sanadiyan murkusheta da jirgin yayi

Akalla mutane hudu ne suka rasa rayukansu a hatsarin da ya afku tsakanin jirgin kasa da adaidaita sahu a safiyar yau Talata, 30 ga watan Afrilu.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 6:45 na safe a Iju Ishaga, unguwan bayan garin Legas.

Yanzu Yanzu: Fasinjoji 4 sun mutu yayinda jirgin kasa ya kara da adaidaita sahu a Lagas

Yanzu Yanzu: Fasinjoji 4 sun mutu yayinda jirgin kasa ya kara da adaidaita sahu a Lagas
Source: Twitter

An tattaro cewa a daidaita sahun mai dauke da fasinjoji ya kafe bayan yunkurin tsallake layin jirgin kasar, wanda hakan yayi sanadiyan murkusheta da jirgin yayi.

KU KARANTA KUMA: Aikin sojoji na haifar da ýaýa masu idanu – Inji Buhari

Legit.ng ta rahoto a baya cewa a watan Janairu, wani hatsarin jirgin kasa ya afku a yankin Mongoro da ke Ikeja, jihar Lagas yayinda daya daga cikin tarragon jigin kasar ya fadi yayiinda yake tafiya, hakan yasa wani jirgin karawa, yayinda fasinjojin ciki suka garkame.

A cewar idon shaida wanda ya wallafa lamarin a shafin zumunta, wasu daga cikin wadanda suka makale a jirgin sunyi kokarin fita ta tagar jiragen da abun ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel