Shugaban Amnesty na Neja-Delta, Charles Dokubo, yana neman hanyar awon gaba da wasu Biliyan 4

Shugaban Amnesty na Neja-Delta, Charles Dokubo, yana neman hanyar awon gaba da wasu Biliyan 4

A wani sautin murya da Darektan kudi na hukumar tsarin Presidential Amnesty na Neja-Delta, ya saki, ya bayyana yadda shugaban hukumar ke faman kokarin sace wasu kudi daga asusun wannan tsari.

Mista Ilem-Iyam ne ya fitar da wannan sauti a Ranar Litinin 29 ga Watan Afrilu inda ya zargi Farfesa Charles Quaker Dokubo da neman daukar Naira Biliyan 4.8 daga asusun gwamnati kafin shugaba Buhari ya kafa sabon gwamnati a Mayu.

Ilem-Iyam, wanda shi ne Darektan kudi a wannan ma’aikata, ya bayyana cewa Mai gidansa Charles Dokubo, da wasu manyan Ma’aikata sun tasa shi gaba da nufin ganin bayansa idan har bai ba su dama sun wawuri kudin da su ke so ba.

KU KARANTA: Takardu sun tonawa babban Ministan Shugaba Buhari asiri

Kamar yadda mu ka samu labari daga SaharaReporters, Farfesa Charles Dokubo, ya kawo wasu kamfanoni 35 da yake so yayi amfani da su wajen bada kwangilolin bogi domin yin sama da fadi da Naira Biliyan 4.88 na hukumar Amnesty.

Wannan Darekta na kudi shi ne ya cije ya hana a zari wadannan Biliyoyi, inda yace ba a bi ka’idojin da su ka dace ba, don haka ya ki sa hannunsa a takardun da ake bukata. Ilem-Iyam, yace ko me zai faru, ba zai fitar da wannan makudan kudi ba.

Darektan yake cewa an yi masa alkawarin Naira Miliyan 150 daga cikin wannan kudi amma yace ba zai ci amana ba. A cewar sa, wannan ya sa aka fara kokarin ganin bayan-sa a wajen aiki, har ta kai ya kai kara wajen jami’an ‘yan sandan kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta karo sababbin taragon jirgin kasa

Iyam, duk yayi wannan bayani ne a fai-fen da ya shigo hannun ‘yan jarida kwanan nan. Charles Dokubo ya musanya duk wannan zargi ta bakin wani Hadiminsa mai suna Murphy Gangana inda yace ana neman bata masa suna ne a wajen aiki.

A jawabin na Gangana yace babu shakka akwai maganar kwangiloli da za a bada masu tsada, don haka ne ma dole aka nemi amincewar hukumar BPP ta sa hannu tukuna, kuma aka yi dace BPP ta amince da kwangilolin, yanzu saura sakin kudin aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel