Ba za mu saurara ba har sai mun kawo karshen ta'addanci - Gwamnatin tarayya

Ba za mu saurara ba har sai mun kawo karshen ta'addanci - Gwamnatin tarayya

- Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta saurara ba har sai ya ga cewar ya cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen ta'addancin Boko Haram a kasar nan

- Shugaban ya ce yanzu haka ana ta samun canje-canje a hukumomin tsaron kasar nan

A jiya Litinin ne 29 ga watan Afrilu shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta ja da baya ba wurin yaki da 'yan ta'addar Boko Haram har sai ta ga bayansu baki daya.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya ta na aiki tukuru wurin ganin komai ya dai daita a kasar nan musamman ma a yankin arewa maso gabas, ya ce gwamnatin na neman goyon bayan 'yan Najeriya wurin ganin ya cika kudurin na sa.

Ba za mu saurara ba har sai mun kawo karshen ta'addanci - Gwamnatin tarayya

Ba za mu saurara ba har sai mun kawo karshen ta'addanci - Gwamnatin tarayya
Source: Twitter

Buhari, wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilta a wurin wani taro a Abuja, ya bayyana cewa dole ne 'yan Najeriya su cire kabilanci da bambancin addini, da kuma siyasa domin yin yaki da ta'addanci a kasar nan.

Ya ce, "Idan zaku tuna a jawabin da na yi lokacin da aka rantsar dani, nayi alkawarin kawo karshen rikicin Boko Haram, wanda ya zama babbar barazana ga al'ummar kasar nan, musamman ma yankin arewa maso gabas. A kokarina na ganin na cika wannan alkawari dana dauka, ana sake koyar da sojojin kasar nan dabarun yaki, sannan ana sayo sababbin makamai, domin karawa sojojin mu karfin gwiwar aiki."

KU KARANTA: Kasashe biyar da suka fi ko ina jin dadin rayuwa, da kasashe biyar da suka fi ko ina kuncin rayuwa

Sannan a kokarin da muke na karfafawa mayakanmu gwiwa, zamu sayo jiragen yaki manya guda biyu, wanda sojojin saman mu za su dinga amfani dasu. Sannan ina mika godiya ta ga rundunar sojin sama ta Najeriya, da irin kokarin da ta yi lokacin babban zabe da aka gabatar a kasar nan.

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Air Marshal Sadique Abubakar, ya ce rundunar sojin saman ta kara daukar ma'aikata 7,500.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel