An kama saurayin nan da ya kashe 'yan uwan budurwarshi su 8 saboda ta ce bata son shi

An kama saurayin nan da ya kashe 'yan uwan budurwarshi su 8 saboda ta ce bata son shi

- Hukumar 'yan sandan jihar Ondo ta yi nasarar cafke saurayin nan da ya kashe 'yan uwan budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi

- Hukumar ta bayyana cewa saurayin ya shigawasan buya da su ne bayan ya aikata laifin, wanda son zuciya da kishi ya kai shi ga wannan aika-aika

Hukumar 'yan sandan jihar Ondo ta kama saurayin nan Deji Adenuga, wanda ta ke nema ruwa a jallo, da zargin sanyawa 'yan uwan budurwarshi mai suna Titi Sanumi wuta, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas daga cikinsu.

Idan ba ku mance ba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton yadda Deji ya sanyawa gidansu budurwarshi Titi Sanumi wuta, saboda ta ce ta gaji da soyayya da shi su hakura gaba daya.

An kama saurayin nan da ya kashe 'yan uwan budurwarshi su 8 saboda ta ce bata son shi

An kama saurayin nan da ya kashe 'yan uwan budurwarshi su 8 saboda ta ce bata son shi
Source: Depositphotos

A cikin fushi, Deji yaje gidan su budurwar ta shi ya zuba man fetur ya kunna musu wuta a lokacin da suke tsakiyar bacci. Rahotanni sun nuna cewa mutane takwas ne suka kone sanadiyyar wutar da Deji ya kunna, sannan mutane biyar sun mutu a take a wurin, inda sauran ukun suka mutu a asibiti.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Dalilan da suka sa zan kai Hadiza Gabon kara kotu - Amina Amal

Bayan yayi aika aikar Deji ya shiga wasan buya shida hukumar 'yan sandan jihar.

Da yake tabbatar da kama saurayin, jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Femi Joseph, ya ce sun kama saurayin da ake zargi da aikata laifin, sannan kuma za su gurfanar da shi a yau Talata 30 ga watan Afrilu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel