Kotu ta yanke ma dillalin wiwi hukuncin kisa ta mummunar hanya

Kotu ta yanke ma dillalin wiwi hukuncin kisa ta mummunar hanya

Wata babbar kotun jahar Anambra dake zamanta a Otuocha ta yanke ma wani dillalin tabar wiwi a jahar, Chukwuebuka Nneji-Olona hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ta kamashi da laifin kisan wani jami’in Dansanda.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kotun ta kama Nneji da laifin kisan Dansanda mai suna Oluwadini Temidayo ta hanyar amfani da falankin katako da duwatsu a kasuwar Oyi dake unguwar Ogbunike cikin karamar hukumar Oyi a shekarar 2014.

KU KARANTA:

Lauya mai kara, Stella Ofokansi ta bayyana ma kotu cewa Dansanda Temidayo baragurbin Dansanda ne, kuma yana yawan zuwa shagunan dillalan wiwi a duk wata don karbar cin hanci, wanda hakan yasa yake rufa musu asiri.

“Amma wata rana sai ya gayyato wasu jami’an Yansanda inda suka diranma shagunan dillalan wiwin bayan bai wuce kwana daya daya je ya amshi cin hancin daya saba karba daga wajensu ba, hakan yayi matukar harzuka dillalan wiwin, inda suka far masa tare da sauran Yansandan.

“Anan ne Nneji ya kashe Dansandan, sa’annan ya ruga zuwa gidan wani boka mai suna Ajana-Oyibo don ya bashi maganin da zai cire masa damuwan kashe Dansandan da yayi, don haka bincike ya tabbatar Nneji ne ya kashe Dansandan a ranar 2 ga watan Mayun 2014, kuma laifin ya saba ma sashi na 274 na kundin hukunta manyan laifuka.” Inji ta.

Daga karshe, Alkalin kotun, mai sharia Amaechina ya bayyana cewa dukkan hujjojin da lauya mai kara ta baje masa sun tabbatar da Nneji ne ya kashe Dansanda, kuma ya gamsu da hakan, don haka ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel