Gwamnatin tarayya ta karyata majalisar dinkin duniya kan yawan al'ummar Najeriya

Gwamnatin tarayya ta karyata majalisar dinkin duniya kan yawan al'ummar Najeriya

- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kiyasin da majalisar dinkin duniya ta yi na cewar yawan al'ummar Najeriya ya kai miliyan 201 ba gaskiya bane

- Gwamnatin tarayyar ta ce majalisar dinkin duniyar ta yi shaci fadi ne kawai

A jiya Litinin ne 29 ga watan Afrilu majalisar dinkin duniya da hukumar kidaya ta Najeriya, suka dan samu banbancin ra'ayi game da yawan mutanen da ke Najeriya.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa yawan mutanen da ke Najeriya ya kai kimanin miliyan 201 a wannan shekarar da muke ciki ta 2019.

Bayan haka kuma, majalisar dinkin duniyan ta ce, yawan haihuwa a Najeriya yana tsakanin kashi 2.6 daga shekarar 2010 zuwa 2019.

Gwamnatin tarayya ta karyata majalisar dinkin duniya kan yawan al'ummar Najeriya

Gwamnatin tarayya ta karyata majalisar dinkin duniya kan yawan al'ummar Najeriya
Source: UGC

A rahoton majalisar dinkin duniyar ta fitar, ya nuna cewa yawan mata masu haihuwa a Najeriya ya ragu da kaso 6.4 a shekarar 1969 zuwa kaso 5.3 a shekarar 2019, hakan na nufin mace a Najeriya ta na haifar akalla yara biyar.

Hakazalika, majalisar ta ce yawan haihuwa a duniya ya kasance kashi 4.8 a shekarar 1969, kashi 2.9 a shekarar 1994 da kuma kashi 2.5 a shekarar 2019.

KU KARANTA: Kasashe biyar da suka fi ko ina jin dadin rayuwa, da kasashe biyar da suka fi ko ina kuncin rayuwa

Rahoton ya nuna cewa matan Najeriya wadanda suke da shekaru 15 zuwa 49 ke yawan samun juna biyu, wadanda sune kaso 19 cikin dari na matan da ke Najeriya.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa yawan al'ummar Najeriya ya karu daga miliyan 54.7 a shekarar 1969 zuwa miliyan 105.4 a shekarar 1994 da kuma miliyan 201 a shekarar 2019.

Rahoton kuma ya nuna cewa, mutane miliyan 88.44 daga cikin miliyan 201 suna tsakanin shekara 0 zuwa shekara 14, yayin da mutane miliyan 64.32 suke tsakanin shekaru 10 zuwa 24.

Sai dai kuma hukumar kidaya ta kasa ta musanta hasashen da majalisar dinkin duniyar ta fitar, inda ta bayyana cewa majalisar ta yi amfani da kiyasi ne da hukumar kidaya ta gabatar a shekarar 2006.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel