Wasu Gwamnoni su na neman a ba su dama su zakulowa Buhari Ministoci

Wasu Gwamnoni su na neman a ba su dama su zakulowa Buhari Ministoci

Daily Trust ta rahoto cewa wasu daga cikin gwamnonin jihohin na kokarin ganin shugaba Muhammadu Buhari ya yi yadda su ka ce wajen zaben wadanda za a ba mukamin Ministocin Najeriya wannan karo.

Wasu Gwamnoni su na neman a ba su dama su zakulowa Buhari Ministoci
Gwamnonin APC za su cusa kan-su a zaben Ministoci Buhari
Source: Facebook

Gwamnoni za su yi kokarin ganin maganar su tayi tasiri a wajen nadin Ministocin wannan karo. A 2015, gwamnoni sai dai su ka ji labarin sunayen Ministoci a gari, don haka za su yi kokarin ganin bana hakan bai sake faruwa ba.

Wasu Gwamnoni sun yi zama na musamman da shugaban kasar a makon da ya gabata a Abuja, bayan ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi zuwa Jordan da Dubai. Jaridar ta fitar da wannan rahoto ne yau, 30 ga Watan Afrilu.

KU KARANTA: Akwai babbar matsala tafe kwan nan - Shugaban Gwamnoni

Kamar yadda labari ya zo mana, an samu gwamna akalla guda daga kowane yanki wajen wannan zama da aka yi da shugaban kasa kafin ya tafi Birnin Landan. Gwamnonin Kudu maso Kudu ne kurum ba su halarci wannan taro ba.

Da farko Gwamnonin sun nemi a ba su dama su kawo wadanda za a ba mukamin Minista daga jihohinsu. Wannan magana dai ba tayi wa wasu gwamnonin APC da su ka sha kasa wajen takarar kujerar Sanata a zaben bana dadi ba.

Wani daga cikin Hadiman gwamnonin kasar ne ya bayyanawa ‘yan jaridar wannan. Hadimin yake cewa daga baya wasu Gwamnoni da su ka kira kan su “Like Minds” sun hada kai, sun sake ganawa da shugaban kasar a kan wannan batu.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar APC ya ja-kunnen Jam’iyyar a kan zaben 2019

Wadannan gwamnoni na jam’iyyar APC su na neman ganin yadda za a dama da su wajen zakulowa shugaba Buhari wadanda su ka cancanta su zama Ministocinsa. Mun ji kishin-kishin din cewa Buhari yayi watsi da wannan tayi na su.

Shugaban kasar ya godewa gwamnonin da su ka kawo masa wannan batu, amma ya nuna masu cewa babu wanda ya isa ya fada masa wanda zai yi aiki da shi, inda kuma yace zai zabo kwararru ne ba tare da la’akari da jam’iyyar mutum ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel