Abin da ya auku a Majalisa a 2015 zai iya maimaita kan sa bana – inji Okafor

Abin da ya auku a Majalisa a 2015 zai iya maimaita kan sa bana – inji Okafor

Labari ya zo mana cewa wani daga cikin masu neman kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya, John Okafor, ya gargadi jam’iyyar APC da cewa, ana yi ganin maiman abin da ya faru a 2015 a bana.

Honarabul John Chike Okafor ya bayyanawa manema labarai cewa jam’iyyar APC tana iya samun kan-ta cikin halin da ta shiga shekaru 4 da su ka wuce wajen zaben shugabannin majalisar tarayya inda aka bijerewa APC mai mulki.

John Okafor wanda yake takarar Kakakin majalisar tarayya yayi wannan jawabi ne a Garin Abuja a Ranar Litinin 29 ga Watan nan na Afrilu. Okafor yayi magana ne a kan sabanin da wasu ‘Yan majalisar APC su ka samu kan-su.

‘Dan Majalisar mai wakiltar yankin jihar Imo yaka cewa duk da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole yana kokarin ganin wadanda yake so sun samu mukamai a majalisar tarayya, zaben da za ayi zai ba kowa mamaki a kasar.

KU KARANTA: INEC ta na kokarin yi wa nasarar Atiku rufa-rufa - PDP

Abin da ya auku a Majalisa a 2015 zai iya maimaita kan sa bana – inji Okafor

John Okafor yana so Ibo su kawo Kakakin Majalisa a 2019
Source: UGC

A cewar Hon. Okafor, Femi Gbajabiamila ya cancanci ya rike majalisar wakilai na tarayya, sai dai ya ja-kunnen jam’iyyar da ta bi a hankali wajen raba kason kujerun majalisar yadda za ayi wa kowane bangare na cikin Najeriya adalci.

Babban ‘dan majalisar na APC yana neman ganin an warewa mutanen Ibo da ke yankin Kudu maso Gabas mukamin Kakakin majalisa. Okafor yace yadda APC ta raba kason majalisa a yanzu, bai da banbanci da abin da tayi a 2015.

A zaben 2015, jam’iyyar APC mai mulki ta nemi a zabi Sanata Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila, sai dai hakan bai yiwu ba inda Bukola Saraki da Yakubu Dogara su ka nuna masu yadda ake wanke allon majalisar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel