Gwamnatin jihar Gombe ta sassauta dokar hana fita a birnin jihar

Gwamnatin jihar Gombe ta sassauta dokar hana fita a birnin jihar

-An sassauta dokar hana zirga-zirga a birnin Gombe, daga 10 na dare zuwa 6 na safe

-Jami'an tsaro a jihar suna nan tsaye kan kafafuwansu domin kwantar da tarzoma

A jiyane gwamnatin jihar Gombe ta sassauta dokar hana fita ta awa 15 da ta sanya a fadin birnin na Gombe. Hakan ya biyo bayan barkewar wani rikici a wani bangaren jihar.

Gwamnatin jihar ta sanya wannan dokar ne ranar Assabar da misalin karfe uku na rana. Hakan ya biyo bayan barkewar rikici a daidai lokacin da ake gudanar da jana’izar wasu yara takwas ‘yan Boys brigade wanda wani jam’in hukumar tsaron masu farin kaya ya kashe.

Gwamnatin jihar Gombe ta sassauta dokar hana fita a birnin jihar

Gwamnatin jihar Gombe ta sassauta dokar hana fita a birnin jihar
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai

Mukaddashin sakataren gwamnatin jihar, James Pisagh ya shaida mana cewa gwamna ya bada umurnin na a mayar da dokar daga kafe 10 na dare zuwa 6 na safe har a sake ganin yanayin garin.

Pisagh ya shawarci jami’an tsaro da su kara jajircewa ganin cewa an samu zaman lafiya mai dorewa a jihar. Ya kuma yi kira ga jama’ar garin das u fita zuwa al’amuransu nay au da kullum kamar yadda suka saba.

Wakilinmu day a zagaya wurare da dama kamarsu tasha, kasuwanni da kuma wasu manya shaguna yace jama’a na nan na gudanar da lamuransu cikin tsanaki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel