An karyata cewa Tinubu na yunkurin sauke Buhari daga kujerar Shugaban kasa

An karyata cewa Tinubu na yunkurin sauke Buhari daga kujerar Shugaban kasa

Wasu kungiyoyi da ake da su masu rajin kare mutunci da martabar damakuradiyya a Najeriya, sun fito sun musanta batun cewa akwai shirin da Bola Tinubu yake yi na ganin an tsige shugaban kasa.

Kungiyar Citizens Watch Nigeria (CWN) da kuma wata mai suna Coalition of Civil Societies and Media Executives for Good Governance in Nigeria wanda aka fi sani da COCMEGG, sun ce babu wani shiri da ake yi na sauke shugaba Buhari.

Wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa rade-radin da ake yi na cewa babban jigon jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu yana da wani boyayyen nufi na tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga kan karagar mulki sam ba gaskiya bane.

KU KARANTA: Shawarar da Gwamnatin Buhari ta yanke a kan harkar tsaro

Shugaban wata kungiya mai suna National Youths Movement, Ishaya Jato, shi ne ya fara yada wannan jita-jita da nufin batawa Bola Tinubu suna kamar yadda kungiyoyin su ka bayyana a wani jawabi da su ka fitar da shi a farkon makon nan.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin Shugaban kungiyar COCMEGG, Omoba Kenneth Aigbegbele da kuma Sakataren kungiyar CWN na kasa watau James Okoronkwo, inda su ka hadu su ka karyata wannan labari, su na kuma kare Bola Tinubu.

KU KARANTA: Takardu sun tonawa wani Minista da Mataimakin Shugaba Buhari asiri

Jawabin na Kenneth Aigbegbele da Okoronkwo ya bayyana Bola Tinubu, a matsayin Dattijon ‘dan siyasa mai son ganin kasa ta cigaba. Su ka kara da cewa, APC ta san irin dawainiya da gudumuwar da Bola Tinubu yake yi mata a fadin kasar nan.

Wadannan kungiyoyi masu zaman kan-su, sun kuma bayyana cewa Bola Tinubu yana yi wa jam’iyyar APC mai mulki da shugaban kasa Muhammadu Buhari cikakken biyayya da mubaya’a. don haka sam ba zai yi abin da jama’a ba za su so ba.

An fitar da wannan jawabi ne a jiya Litinin 29 ga Watan Afrilu inda har aka kawo misalin irin gwagwarmayar da Bola Tinubu yake yi wajen ganin gwamnatin Buhari ba ta kara farashin man fetur ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel