Zaben gwaman Kogi: Shugabannin APC sun nuna rashin amincewarsu akan sake tsayawa takarar Bello

Zaben gwaman Kogi: Shugabannin APC sun nuna rashin amincewarsu akan sake tsayawa takarar Bello

-Akwai kallo bana! zaben gwamnan jihar Kogi dake tafe ko wa APC zata tsaida?

-Jiga-jigan yan jam'iyar APC a Kogi basu tareda Yahaya Bello a zabe mai zuwa

Masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC sun rubutawa shugaba Buhari inda suke neman da a hana Yahaya Bello damar tsayawa takarar gwamna a karo na biyu.

A cewarsu, gwamnan ya samu tallafin kudi daga wurin gwamnatin tarayya na naira biliyan 244 cikin shekaru uku da suka gabata, sai dai kuma bai aikata komi da wannan tallafin ba.

Zaben gwaman Kogi: Shugabannin APC sun nuna rashin amincewarsu akan sake tsayawa takarar Bello

Zaben gwaman Kogi: Shugabannin APC sun nuna rashin amincewarsu akan sake tsayawa takarar Bello
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai

A halin yanzu wannan gwamnan ya rike albashi, fansho da kuma kudin sallamar ma’aikata na jihar, duk da haka kuwa babu wani gagarumin aiki na zo a gani da yayi ko yake kan yi a jihar.

Sun bayyana gwamnan a matsayin wanda bai tabuka komi. Takardar tasu ta samu sa hannun jagoran APC a Kogi sanata Alex Kadiri.

“ Ba mutanen Kogi bane suka zabi Yahaya Bello. Mutuwar Abubakar Audu ce ta bashi damar kasancewa gwamana. Ya kuma nuna ma kowa cewa shi baida ingancin kasancewa jagoran wannan jihar tamu a matsayin gwamna.

“ Muna rokonka na ka janye goyon bayanka daga wurin Yahaya Bello a matsayin dan takarar gwamna a zabe mai zuwa a jihar Kogi.

“ Idan ko har jam’iyar APC ta tsaida shi a matsayin dan takarar to ko shakka babu zamu rasa wannan jiha zuwa ga jam’iyar adawa.” abinda takardar ta kunsa kenan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel