Karin bayani: Yadda yan bindiga suka yi awon gaba da babban jigo a gwamnatin Buhari

Karin bayani: Yadda yan bindiga suka yi awon gaba da babban jigo a gwamnatin Buhari

A ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu ne labari ya watsu cewa wasu gun yan bindiga sun yi awon gaba da wani babban aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma shugaban hukumar ilimi ta bai daya UBEC, Dakta Muhammad Mahmood.

Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne da yammacin Litinin, amma daga bisani rundunar Yansandan Najeriya tayi karin haske game da yadda lamarin ya auku, inda rundunar tace da misalin karf 3:30 na rana ne yan bindigan suka tare motar Muhammed.

KU KARANTA: Ke duniya: Matashi ya kashe mahaifinsa, ya babbaka gawarsa

Karin bayani: Yadda yan bindiga suka yi awon gaba da babban jigo a gwamnatin Buhari

Muhamamd da diyarsa
Source: UGC

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kaduna, DSP Yakubu Abubakar Sabo ne ya bayyana haka da daren Litinin, inda yace yan bindiga sanye da kayan Sojoji ne suka tare wata babbar Mota kirar Land Cruiser tare da bude mata wuta, motar da Muhammad yake ciki tare da diyarsa.

“A yau 29/04/2019 mun samu bayani daga DPO na yansandan yankin Katari cewa da misalin karfe 3:30 na rana aka kirashi aka labarta masa cewa yan bindiga sanye da kayan Sojoji sun kama wata mota kirar Land Cruiser mai lamba 07E04 FG, da wata Toyota Sieena mai lamba SLJ 465 TN a daidai kauyen kurmin Kare dake kan titin Kaduna zuwa Abuja.

“Yan bindigan sun bude ma motocin wuta ne, wanda hakan ya sabbaba mutuwar direban motar Muhammad, daga nan suka tasa keyar Muhammad da diyarsa, yayin da mutanen dake cikin motar Sienna, Alowonle Olalere, da Onuka Victor suka tsira a dalilin dauki da Yansanda suka kai musu.

Karin bayani: Yadda yan bindiga suka yi awon gaba da babban jigo a gwamnatin Buhari

Buhari tare da Muhammad daga hannun dama
Source: Facebook

“Alowonle da Onuka yarbawa ne mazauna garin Ibadan na jahar Oyo ne, kuma suna kan hanyarsu ta komawa gidane daga jahar Kano inda suke shirya wani Fim mai suna “The Last step”, sun tsira, amma sun samu rauni.

“Hadakar Yansandan kwantar da tarzoma, sashin yaki da masu garkuwa, Sojoji na musamman tare da Operation Yaki duk sun bazama don farautar yan bindigan a cikin dajin da nufin ceto Muhammad da diyarsa, zuwa yanzu an mika motocinsu zuwa ofishin Yansanda.” Inji shi.

Daga karshe sanarwar ta kara da cewa kwamishinan Yansandan jahar Kaduna, Ahmad Abdulrahman ya nemi jama’a su taimaka musu da bayanai da zasu kaisu ga kama maharan, sa’annan yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen rage ayyukan miyagu a Kaduna ba.

Shi dai Muhammad aminin shugaba Buhari ne kuma abokin siyasarsa, inda ya taba zama dan majalisar wakilai mai wakiltar Kaduna ta kudu daga shekarar 2003 zuwa 2007, haka zalika Buhari ya nadashi babban hadiminsa a farkon wannan gwamnati, daga bisani ya nadashi shugaban UBEC.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel