An fara kamen karuwai a jihar Kano saboda azumi

An fara kamen karuwai a jihar Kano saboda azumi

- Karuwai masu zaman kansu a jihar Kano suna ganin ta kansu, yayin da hukumar Hisbah ta sha alwashin kamesu kafin zuwan watan Ramadana

- Hukumar ta tilastawa da yawa daga cikin karuwan barin fadin jihar

Hukumar Hisbah ta jihar Kano tayi kamen mata masu yawan gaske, wadanda suke zaman kansu a fadin jihar, ta yi kamen ne bisa dalilinta na tsaftace jihar kafin zuwan azumin watan Ramadan.

Hukumar ta yi kamen ne a wani sumame da ta kai zuwa gidajen da ake tara mata masu zaman kansu a cikin birnin Kano dama wasu kananan hukumomi da ke fadin jihar.

An fara kamen karuwai a jihar Kano saboda azumi

An fara kamen karuwai a jihar Kano saboda azumi
Source: UGC

Shugaban hukumar Hisba na jihar Kano Malam Abba Sufi, ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar ta kama mata Karuwai kimanin guda 26 a cikin birnin Kano kawai, ya kara da cewa yanzu haka an gurfanar dasu a gaban kotun shari'ar musulunci domin yanke musu hukunci.

"Kotu ta yanke musu hukunci zaman gidan kaso na shekara daya, akan dokar hana karuwanci a fadin jihar," in ji shi.

Shugaban ya bayyana cewa, sun kuma kai wani sumame kananan hukumomin Dawakin Kudu da Tamburawa, wadanda suka yi kaurin suna wurin tara mata karuwai.

KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Dalilan da suka sa zan kai Hadiza Gabon kara kotu - Amina Ama

Sai dai kuma hukumar ta ce, matan da ta kama a dawakin kudu ta sake su bayan sunyi yarjejeniya akan cewar za su bar fadin jihar.

Shugaban Hisban ya ce Kano jiha ce dake koyi da addinin musulunci, wacce kuma ke bin shari'ar musulunci, saboda haka hukumar zata cigaba da kokari wurin ganin ta kawo karshen dukkanin karuwan dake fadin jihar kafin zuwan azumin watan Ramadana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel