Lantarki bai kai 8000MW megawatt kamar yadda Gwamnatin Buhari ta ke ikirari ba

Lantarki bai kai 8000MW megawatt kamar yadda Gwamnatin Buhari ta ke ikirari ba

Karfin wutar lantarkin Najeriya ya zazzago daga megawatts 4000 zuwa kusan 2000 a halin yanzu. A cikin Watan Fubrairu ne Ministan wuta da gidaje da ayyuka, Babatunde Fashola, yace wuta ya karu.

A wancan lokaci, Babatunde Raji Fashola, yayi ikirarin cewa wutar lantarki ya karu da 100% a Najeriya a cikin shekaru 3 da shugaba Buhari yayi yana mulki. Shi ma mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya taba fadan irin wannan magana.

A watan nan na Afrilu, Farfesa Yemi Osinbajo, ya fito ya fadawa Duniya cewa lantarkin da Najeriya ta ke ja ya tashi daga megawatt 4000 zuwa fiye da megawatt 8000. Sai dai bincike ya nuna cewa wannan magana ko kadan ba gaskiya bane.

KU KARANTA: Dole a zage dantse wajen neman kudin shiga - Gwamnatin Najeriya

Wani rahoto da aka ba fadar shugaban kasa ta hannun matimakin shugaban kasar ya nuna akasin abin da gwamnatin Buhari ta ke fada. Jaridar Vanguard tace a cikin Watan nan na Afrilu, karfin wuta yayi kasa sosai bayan an samu wasu cikas.

Rahoton da aka ba mataimakin shugaban kasar yana cewa a Ranar 23 ga Watan Afriku, lantarkin da aka raba bai wuce 87, 061MW ba. Wannan rahoto da Vanguard ta bankado ya nuna cewa abin da aka samu duka-duka bai haura megawatt 2093 ba.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP tace an wawuri N14tr a mulkin Shugaba Buhari

Rahoton ya nuna cewa Najeriya ta rasa fiye da megawatt 2048 na wutar lantarki a Ranar Talatar da ta gabata. An samu wannan matsaloli ne bayan da bangaren kamfanin NNPC da ke kula da sha’anin gas ya gaza kammala aikin da yake yi.

Haka zalika kamfanonin da ke tatso wuta irin su Egbin, Omotosho, Olorunsogo da kamfanin Paras duk sun gaza samar da wutan da za a rabawa kamfanonin DISCO masu kai wutan ga mutane, Hakan ya bayu ne da fashewar wata hanyar gas.

A Ranar 25 ga Watan nan na Afrilu ne lamarin wutan ya tabarbare gaba daya inda tashoshi 4 da ake da su masu bada wuta su ka dauke aiki. Wannan ya tabbatar da cewa batun cewa ana samun mega watt 800 a rana a kasar ba gaskiya bane a yanzu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel