Dalilin da yasa bazan bar APC ba, inji gwamnan Kogi

Dalilin da yasa bazan bar APC ba, inji gwamnan Kogi

-Babu rashin jituwa a reshen jam'iyar APC na Kogi, inji Yahaya Bello

-A dalilin jajircewata ne muka samu gagarumar nasara da muka samu a zabukan da suka gabata, inji gwamnan Kogi

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yace har yanzu shi dan jam’iyar APC ne kana kuma babu rashin jituwa a reshen jam’iyar na jihar.

Bello ya shaidawa manema labarai hakan ne yayinda ya halarci wani taron bitar aiki da aka shirya a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa domin sabbin gwamnoni da kuma wadanda zasu koma karo na biyo.

Dalilin da yasa bazan bar APC ba, inji gwamnan Kogi

Dalilin da yasa bazan bar APC ba, inji gwamnan Kogi
Source: Facebook

KU KARANTA:Rundunar sojin kasa zata tanadi N1bn domin ababen hawa, inji Buratai

Yace sabbin da kuma tsoffin gwamnoni da zasu sake komawa karo na biyu na da bukatar wannan bita saboda su shiryawa kalubalen dake gabansu.

“ Ni dai abinda zan iya cewa akan jihata shine babu rashin jituwa tsakanin ‘yan APC a Kogi.

“ Manya mutane da kuma masu ruwa da tsaki sun san da cewa reshen APC na jihar Kogi na nan kalau babu rashin jituwa a tsakanin mambobi. Dalilin hakan ne ya sanya jam’iyarmu tayi nasara a zaben shugaban kasa a Kogi.

“ Bugu da kari, munyi nasarar lashe kujeru biyu daga cikin uku na majalisar dattawa, mun kuma lashe 7 daga cikin kujerun majalisar wakilai 9. Sannan kuma a karo na farko a jihar kogi jam’iyar APC ta lashe gaba daya kujeru 25 na majalisar dokokin jihar.

“ Idan akwai rashin jituwa babu yadda za’ayi mu samu wannan gagarumar nasara. Don haka ina so in sake jaddada muku cewa har yanzu ina nan a APC, hasalima sake karfafa jam’iyar da nayi a jihar shi ya kaimu zuwa wannan nasara.” inji Bello.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel