Atiku: INEC ta fara canja bayanan kan na'urorinta dake ofisoshin jihohi - PDP

Atiku: INEC ta fara canja bayanan kan na'urorinta dake ofisoshin jihohi - PDP

Babbar jam'iyyar hamayya, PDP, ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da canja bayanan sakamakon zaben shugaban kasa na shekarar 2019 dake kan na'urorinta.

A jawabin da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, ya fitar a ranar Litinin, ya ce a kokarinta na canja sakamakon zaben shugaban kasa na gaskiya, hukumar INEC ta fara canja bayanan kan na'urori masu kwakwalwa dake shedikwatar ta da na sauran jihohi bayan ta riga ta aika sakamako na gaskiya da farko.

"Yanzu haka INEC na canja bayanan dake kan na'urorinta a shedikwatar hukumar da na sauran jihohi don kawai ta canja sakamakon zaben shugaban kasa na gaskiya da ta aika da farko daga mazabun dake fadin kasar nan," a cewar Ologbondiyan.

Sakataren yada labarn ya kara da cewa INEC ta dauko hayar wasu kwararru a bangaren goge bayanai daga kan na'ura mai kwakwalwa domin su yi mata aikin canja sakamakon zaben.

Sannan ya cigaba da cewa; "jam'iyyar mu na da cikakken bayani a kan yadda INEC da fadar shugaban kasa suka hada kai wajen kwararru a goge bayani a kan na'ura mai kwakwalwa domin su canja sakamakon zabe na gaskiya dake kan na'urorin hukumar a hedikwatar ta kuma na jihohi."

Jam'iyyar PDP ta kara zargin INEC da daukan wasu kwararrun da zasu canja rijistar masu zabe domin kara boye irin magudin da aka tafka a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.

Sakataren yada labaran ya bayyana cewar PDP za ta dauko kwararru a bangaren gudanar da gwaji ta hanyar amfani da kimiyyar zamani domin su duba dukkan kayan aikin da aka yi zaben shugaban kasa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel