Sojan da aka sace tare da iyalinsa sun samu 'yanci

Sojan da aka sace tare da iyalinsa sun samu 'yanci

Wani babban soja a rundunar soji ta kasa da wasu 'yan bindiga suka sace tare da iyalinsa ranar Lahadi a kan hanyar Wukari zuwa a jihar Taraba sun samu 'yanci.

Majiya da dama daga kananan hukumomin Wukari da Ibbi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewar 'yan bindigar sun saki sojan da iyalinsa a daren ranar Lahadi.

Majiyar mu ta shaida mana cewar 'ya sanda da sojoji sun yiwa kauyen Ibiwa, inda aka sace sojan, tsinke a ranar Lahadi.

Sojojin, kamar yadda wata majiya ta fada, sun bayar da wa'adin sa'o'i 24 ga mutanen kauyen a kan a fito da jami'in sojan tare da iyalinsa da aka sace.

Daga cikin wadanda suka shiga sahun jami'an tsaro wajen neman sojan da iayalinsa har da shugaban karamar hukumar Ibbi da babban basaraken karamar hukumar.

Sojan da aka sace tare da iyalinsa sun samu 'yanci

Dakarun soji
Source: Twitter

Sai dai, wata majiya ta bayyana cewar 'yan binigar sun saki sojan da iyalinsa bayan shugaban karamar hukumar Ibbi ya bayar da kudin fansa.

Rundunar soji ba ta sanar da cewar ta kama kowa dangane da batun sace sojan da iyalinsa ba, sai dai ta tabbatar da cewar sojan da iyalinsa sun samu 'yanci.

DUBA WANNAN: An sace shugaban hukumar UBEC tare da diyar sa a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Taraba, DSP David Misal, ya ce ba zai yi magana a kan abinda ya shafi rundunar soji ba.

"Ba na son a fadi wani abu da ya shafi rundunar soji da suna na. Wannan abu ne da ya shafi zallar aikin rundunar soji," a cewar Misal

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel