Hukumar 'yan sanda ta cafke masu tayar da zaune tsaye 264 a jihar Anambra

Hukumar 'yan sanda ta cafke masu tayar da zaune tsaye 264 a jihar Anambra

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Anambra, a ranar Litinin ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke miyagun mutane 264 masu tayar da zaune tsaye da zartar da ta'addanci daga ranar 1 ga wata Afrilu kawowa yanzu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, cikin wadanda hukumar ta cafke sun hadar da kasurguman 'yan ta'ada da suka kulla kutungwilar wasu munanan ta'addanci biyu na garkuwa da kashe-kashen al'umma a fadin jihar.

Hukumar 'yan sanda ta cafke masu tayar da zaune tsaye 264 a jihar Anambra
Hukumar 'yan sanda ta cafke masu tayar da zaune tsaye 264 a jihar Anambra
Source: UGC

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mustapha Danduara, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata hira yayin ganawar sa da manema labarai a hedikwatar hukumar 'yan sanda ta Amawbia daura da birnin Awka.

A cewar sa cikin adadin miyagun mutane da hukumar ta cafke, akwai 231 a suka yi kaurin suna wajen ta'adar kungiyar asiri, 'yan fizge 16, masu kwancen mota 4, masu garkuwa da mutane 3 da kuma manyan 'yan fashi da makami goma.

KARANTA KUMA: Hukumar sojin saman Najeriya ta cika shekaru 55 da kafuwa

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar ta samu nasarar cafke masu aikata mummunar ta'adar tare da hadin gwiwar rassan yaki da miyagun ababe na hukumomin tsaro da dama da ke fafutikar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma a fadin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel