Rikicin kabilanci: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 5 a Ribas

Rikicin kabilanci: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 5 a Ribas

Rundunar 'yan sanda a jihar Ribas ta tabbatar da mutuwar mutane biyar a wani sabon harin 'yan bindiga da aka kai ranar Lahadi a wasu kauyuka biyu a karkashin karamar hukumar Obio/Akpor.

An kai harin ne a kan mazauna garin Rumukwurusi da na Eneka.

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar tsafi ne suka bude wuta a wani wurin kallon wasan kwallon kafa a garin Eneka dake karkashin karamar hukumar Obio/Akpor, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyar da suka hada da wata mace guda daya.

Wani shaidar gani da ido ya shaida wa majiyar mu cewar 'yan bindigar sun zo a wata mota kirar 'Toyota Avalon' suna neman wani mutum.

Jin haushin basu samu wanda suka zo nema ba ne yasa suka bude wuta a wurin kallon kwallon da wasu ke gasar shan giya.

Rikicin kabilanci: 'Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum 5 a Ribas

Gwamnan jihar Ribas; Nyesom Wike
Source: Depositphotos

Rahotanni sun bayyana cewar kafin 'yan bindigar su karaso garin Eneka, sai da suka biya ta garin Rumukwurusi a yankin karamar hukumar ta Obio/Akpor, inda suka kashe wata dalibar shekarar karshe a jami'a.

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun dawo hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun sace mutane 12

Da yake tabbatar da labarin kai harin, kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya ce duk da basu kama kowa ba dangane da kai harin, rundunar 'yan sanda ta samu muhuimman bayanai da zasu taimaka musu wajen binciken da suke yi.

Kazalika, ya bayyana cewar, a 'yan kwanakin baya bayan nan, jihar na fama da matsalar yawaitar kai hare-hare a kan al'umma da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ke kai wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel