EFCC tayi karin haske a kan yunkurinta na sake gurfana da zababben gwamnan Bauchi

EFCC tayi karin haske a kan yunkurinta na sake gurfana da zababben gwamnan Bauchi

Rashin zuwan Jastis Yusuf Haliru, alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja ya kawo cikas a sauraron karar da hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta shigar da zababben gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Mohammed, zababben gwamnan jihar Bauchi a karkashin tutar jam'iyyar PDP, a kan wasu sabbin tuhume-tuhume guda shida da suka hada da bayar da kiyasin dukiya na karya da kuma bawa hukumar EFCC bayanan bogi.

Muhammed da lauyoyinsa da kuma lauyoyin hukumar EFCC sun halarci zaman kotun amma kasancewar alkalin kotun ya tafi aiki na musamman a kotun sauraren karar zabe a jihar Ogun, ba a samu damar fara sauraron karar ba.

Da yake magana da manema labarai a harabar kotun, lauyan hukumar EFCC, Wahab Shittu, ya ce; "hukumar EFCC na yaki ne da cin hanci, a saboda haka ba ruwanta da siyasa".

EFCC tayi karin haske a kan yunkurinta na sake gurfana da zababben gwamnan Bauchi

Bala Mohammed; zababben gwamnan Bauchi.
Source: Twitter

"Ita jama'a take yiwa aiki."

A kan batun gurfanarwar, ya ce; "magana ce a gaban babban alkalin kotu wacce muka dade da shigar wa.

DUBA WANNAN: Buhari ya bayar da umarnin sakin 'yan Najeriya 3 da hukumar Saudiyya ta kama

"A cikin satin da ya gabata muka samu kira daga wannan kotu cewar ta tsayar wannnan rana domin fara sauraron karar, a saboda haka mu gurfanar da wanda muke kara."

Ya kara da cewa bangaren shari'a zai nada wani sabon alkalin da zai cigaba da kula da karar.

Kazalika, ya bayyana cewar kar wasu su dauka cewar hukumar EFCC na kokarin yin barazana ga wani mutum ne.

"Ita kotu ba ta wani ba ce, ta na yin aiki ne domin kowa da kowa," a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel