Dole jihohi su inganta hanyoyin samar da kudin shiga a Najeriya - Osinbajo

Dole jihohi su inganta hanyoyin samar da kudin shiga a Najeriya - Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya cebukata a halin yanzu ta sanya dole jihohin Najeriya su bunkasa hanyoyin samar da kudaden shiga da kuma karbar haraji cikin shekaru kadan masu gabatowa.

Farfesa Osinbajo ya yi wannan kira a ranar Litinin yayin halartar taron budar kai na sabbin zababbun gwamnoni da masu dawowa bisa kujerar mulki da aka gudanar a babban dakin taro na Banquet da ke fadar shugaban kasa ta Villa a garin Abuja.

Shugaban kasa Buhari tare da mataimakin sa, Farfesa Osinbajo

Shugaban kasa Buhari tare da mataimakin sa, Farfesa Osinbajo
Source: UGC

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, taron wanda kungiyar gwamnonin Najeriya bisa jagorancin shugaban ta, gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari ta gudanar, ya samu halarcin gwamnonin Najeriya na da da kuma na yanzu da sauran masu ruwa da tsaki ta fuskar jagoranci.

A yayin da ya kasance al'ada ga sabbin zababbun shugabanni su yi koken rashin kudi a baitul malin da suka taras, mataimakin shugaban kasar ya ce dole ne su yi hobbasa wajen inganta hanyoyin samar da kudin shiga domin inganta jin dadin al'ummomin su.

KARANTA KUMA: Za a sake shiga matsin tattalin arziki a Najeriya nan ba da jimawa ba - Gwamna Yari

Da yake ci gaba da wayar da kai ga sabbin gwamnoni, Farfesa Osinbajo ya nemi su yi koyi da gwamnatin jihar Legas sakamakon zarra da ta yiwa sauran jihohin Najeriya ta fuskar samar da kudin shiga domin bunkasa ci gaban al'ummar ta.

Cikin nasa jawaban gwamna Yari na jihar Zamfara ya nemi jagorori da su kauracewa cin bashi a kasar nan, inda a cewar sa hakan ba zai taba kawo karshen kalubalai na matsin tattalin arziki da ta ke fuskanta ba a yanzu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel