Masu garkuwa sun dawo hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun sace mutane 12

Masu garkuwa sun dawo hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun sace mutane 12

Wasu tsagerun masu garkuwa da mutane sun dawo hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da yin awon gaba da matafiya da dama, kamar yadda jarudar Daily Nigerian ta rawaito.

Wani shaidar gani da ido, Mohammed Dambatta, wanda ya sha da kyar, ya shaida wa majiyar jaridar cewar masu garkuwa da mutanen sun sace mutane da dama a daidai Kurmin Kare a karamar hukumar Kachia dake jihar Kaduna da misalin karfe 3:00 na ranar Litinin.

A cewar sa, masu garkuwa da mutanen sun yi harbin iska a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, lamarin da ya saka a kalla motoci 15 suka tsaya, wanda hakan ya bawa masu garkuwa da mutanen damar tafiya da mutane da dama zuwa cikin daji.

Masu garkuwa sun dawo hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun sace mutane 12

'Yan sandan Najeriya
Source: Depositphotos

"Na kidaya a kalla motoci 15 wadanda aka sace muatanen ciki, a cikin motocin har da ta 'yan sanda da motar safarar mutane mallkar gwamnatin jihar Kano (Kano Line) da kuma wata mota kirar 'Jeep'," a cewar sa.

DUBA WANNAN: Buhari ya bayar da umarnin sakin 'yan Najeriya 3 da hukumar Saudiyya ta kama

A satin da ya gabata ne babban sufeton rundunar 'yan sanda na kasa (IGP), Abubakar Adamu, ya bayyana cewar hanyar Abuja zuwa Kaduna tayi lafiya bayan kaddamar da wani atisaye mai taken 'Puff Arder" domin yaki da miyagun aiyukan, musamman matsalar sace matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel