PDP da APC: Kotun zabe na Kano ta sanya 6 ga watan Mayu ranar sauraron shari’a

PDP da APC: Kotun zabe na Kano ta sanya 6 ga watan Mayu ranar sauraron shari’a

Kotun saurararon kararrakin zaben gwamna na jihar Kano ta sanya ranar 6 ga watan Mayu domin fara sauraron karan da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta suka shigar akan Gwamna Abdullahi Ganduje da jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

A cewar jaridar Daily Trust,lauyan PDP da dan takararta Abba Kabiru Yusuf, Barista Bashir Yusuf Muhammad, yace sun shigar da kararraki biyu bias ga ci gaban da aka samu baya-bayan nan.

A nashi martanin, lauyan APC da Gwamna Ganduje, Barista Musa Abdullahi Lawal, ya bayyana cewa hukuncin kotun yayi daidai.

PDP da APC: Kotun zabe na Kano ta sanya 6 ga watan Mayu ranar sauraron shari’a

PDP da APC: Kotun zabe na Kano ta sanya 6 ga watan Mayu ranar sauraron shari’a
Source: UGC

Alkalin da ke jagorantar zaman, Justis Halima Shamaki ta dage zaman zuwa ranar 6 ga watan Mayu domin ci gaba da zama.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Arewa ta marawa Saraki baya, ta caccaki Tinubu da kungiyar Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta nemi kotun da ke sauraron karar zaben 2019 a jihar Kano, da ta bayyana cewa ita ce ta lashe zaben gwamna da aka yi a maimakon Abdullahi Umar Ganduje.

Jam’iyyar tana nema kotu ta soke nasarar da gwamna mai-ci Dr. Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC mai mulki ya samu a zaben na bana. PDP tana so ne a ba ‘dan takararta, Injiniya Abba K. Yusuf nasara a zaben na 2019.

Lauyoyin PDP sun fadawa kotun karar zaben cewa ‘dan takarar ta na 2019, Abba Kabiru Yusuf, ya samu kuri’un da ake nema wajen lashe zaben gwamna don haka ta nemi a tsaida sa a matsayin zababben gwamna na jihar Kano.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel