Buhari yayi umurnin sakin Zainab Aliyu da hukumar Saudiya ta kama kan safarar miyagun kwayoyi

Buhari yayi umurnin sakin Zainab Aliyu da hukumar Saudiya ta kama kan safarar miyagun kwayoyi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci babban alkalin tarayyar Najeriya, Abubakar Malami, da ya tallafa wajen sakin Zainab Aliyu, wata daliba da aka kama bisa kuskure kan safarar miyagun kwayoyi a kasar Saudiyya.

Hukumomin kasar Saudiyya ta kama Zainab wacce ta kasance dalibar jami’ar Maitama Sule, Kano, a ranar 26 ga watan Disamban 2018 kan zargin tafiya da jaka mai dauke da kayayyakin da aka aka haramta wato tramadol.

Wacce ake zargin tayi tafiyar ne ta filin jirgin Mallam Aminu Kano, MAKIA, don aikin umurah tare da mahaifiyarta Maryam da kuma yar’uwarta Hajara.

Buhari yayi umurnin sakin Zainab Aliyu da hukumar Saudiya ta kama kan safarar miyagun kwayoyi

Buhari yayi umurnin sakin Zainab Aliyu da hukumar Saudiya ta kama kan safarar miyagun kwayoyi
Source: Twitter

Hadimin Shugaban kasa, Bahir Ahmad ya bayyana a ranar Litinin, 29 gaa watan Afrilu cewa tuni gwamnatin tarayya ta umurci ministan shari’a da ya tabbatar da sakinta sannan a dawo da ita gida Najeriya.

KU KARANTA KUMA: PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin kasar Saudiya ta tabbatar da zartuwar hukuncin kisa kan wasu Mutane 37 da su ka aikata laifuka daban-daban masu nasaba da ta'addanci kamar yadda Ministan harkokin cikin gida na kasar ya bayyana.

Mutane 37 da su ka kasance 'yan asalin kasar Saudiya an zartar masu da hukuncin kisa sakamakon miyagun laifukan da suka aikata masu nasaba da ta'addanci kama daga ra'ayin rikau, kai hari tare da hallaka jami'an tsaro, da sauran dangin laifuka na ta'addanci.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel