Buhari ya bayar da umarnin sakin 'yan Najeriya 3 da hukumar Saudiyya ta kama

Buhari ya bayar da umarnin sakin 'yan Najeriya 3 da hukumar Saudiyya ta kama

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan shari'a, Abubakar Malami, da ya tabbatar da cewar hukumomin kasar Saudiyya sun saki matashiyar nan yar Najeriya, Zainab Aliyu, da aka yi kuskuren kama wa bisa zargin laifin safarar kwaya.

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama Zainab, daliba a jami'ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da kwayar 'tramol' zuwa kasar Saudiyya.

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin 'umra' tare da mahaifiyarta, Maryam, da 'yar uwarta, Hajara.

Babbar mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren harkokin da suka shafi kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ce ta sanar da umarni da shugaba Buhari ya bayar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, ta kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara tattauna batun sakin Zainab tare da wasu mutane biyu dake da irin matsalar da Zainab ta samu.

Buhari ya bayar da umarnin sakin 'yan Najeriya 3 da hukumar Saudiyya ta kama

Zainab
Source: Twitter

"Shugaban kasa Muhammadu Buharu ya umarci ministan shari'a ya dauki matakan da suka dace a kan matsalar matashiyar. Mun fara tattauna wa da hukumomin kasa, za ta dawo gida tare da wasu mutane biyu dake da irin wannan matsala," kamar yadda Dabiri ta sanar a shafinta na Tuwita.

DUBA WANNAN: Sufuri: FG ta duba lafiyar karin jirage 64 da za ta sayo daga kasar China

Mahaifin Zainab ne ya fara rubuta wata takardar korafi da ya aika wa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan zargin cewar an saka kwaya a jakar diyar sa.

Daga bisani, binciken NDLEA ya gano cewar akwai gungun wasu ma'aikan kamfanonin jirgin sama da suka kware wajen yin cushen kwayoyi a jakankunan matafiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel