Sufuri: FG ta duba lafiyar karin jirage 64 da za ta sayo daga kasar China

Sufuri: FG ta duba lafiyar karin jirage 64 da za ta sayo daga kasar China

Gwamnatin tarayya ta duba lafiyar karin sabbin jiragen kasa 64 da ake kera mata a kasar China, wadanda ake sa ran za a kawo wasu daga cikinsu Najeria a watan Yuni. Za a kara 10 daga cikin sabbin jrage a jigilar mutane daga Abuja zuwa Kaduna.

A sanarwar da Mohammed Idris, darektan yada labarai a ma'aikatar sufuri, ya fitar ranar Litinin a Abuja, ya ce ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ne ya jagoranci tawagar wakilan gwamnatin tarayya zuwa kamfanin 'Chinese Railway Rolling-stock Corporation (CRRC)' domin ganin yadda aikin kera jiragen ke tafiya da kuma matakin da ake kai a hanlin yanzu.

Amaechi ya ce Najeriya na sa ran karbar rukunin jirage 10 na farko a watan Yuni domin rage cunkuso wajen jigilar mutane daga Abuja zuwa Kaduna.

A cewar sa, "mu na bukatar karin sabbin jiragen kasa zuwa watan Yuni. Mu na bukatar karin jiragen ne domin saukaka jigilar mutane, a saboa haka mu na bukatar 10 daga cikin sabbin jiragen 64.

Sufuri: FG ta duba lafiyar karin jirage 64 da za ta sayo daga kasar China

Amaechi da tawagar gwamnatin tarayya a kasar China
Source: UGC

"Mu na neman guda 10 ne a halin yanzu domin inganta harkar sufurin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna, mu na matukar bukatar su domin saukaka cunkuson da ake samu a tashoshin jiragen kasa na Abuja da Kaduna.

"Kwanan za a kammala aikin digar jirgin Lagos zuwa Ibadan, mu na sa ran ragowar jiragen za su kammala kafin lokacin. Amma dai yanzu mu na bukatar guda 10 kafin su kammala ragowar.

DUBA WANNAN: Saraki ya samu gundumemen mukami a hukumar IHRC ta kasa da kasa

Kazalika, Amaechi ya bayyana cewar aikin kera jiragen ba ya sauri tare da yin kira ga kamfani da ke yin aikin da su kara hanzari don kar lokacin da aka deba wa kwangilar ya kure.

"Aikin ba ya sauri gaskiya, duk da ba mu biya dukkan kudin aikin kwangilar ba, amma mun biya wani kaso mai tsoka daga cikin kudin aikin. A saboda haka akwai bukatar su kara hanzari a kan aikin," a cewar Amaechi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel