Saraki da Tinubu na fada ne don son juya majalisar dokokin kasa – Shehu Sani

Saraki da Tinubu na fada ne don son juya majalisar dokokin kasa – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani yace musayar kalamai dake gudana tsakanin Bola Tinubu da shugaban majalisa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya kasance muradin bangarorin na son juya akalar jagorancin majalisar dokokin kasar.

Dan majalisan mai wakiltan yankin Kaduna ta Tsakiya a majalisar dokokin kasar a shafin sa na zumunta a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu ya bayyana cewa musayar kalaman da ke wakana a tsakanin yan siyasan ya kasance cigaban abunda ya faru a majalisa.

Haka zalika, takaran shugabancin majalisar kasa mai jiran gado ya dauki wani salo kamar yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki alhakin neman goyon bayan yan majalisa ga Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila.

Saraki da Tinubu na fada ne don son juya majalisar dokokin kasa – Shehu Sani

Saraki da Tinubu na fada ne don son juya majalisar dokokin kasa – Shehu Sani
Source: UGC

Sanata Ahmad Lawan na son ya zama shugaban majalisa, yayin da Honorable Femi Gbajabiamila ke da ra’ayin zama kakakin majalisan wakilai.

KU KARANTA KUMA: PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya

Jaridar Nation ta rahoto cewa majiya masu inganci sun ce shugaban kasar bai dauki komai ba da wasa ganin baya son a maimaita abunda ya faru a 2015.

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, wata kungiya mai suna Arewa Youth for Peace and Security (AYPS), ta yabi shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki akan shugabancinsa a majalisar dokokin kasar, wanda tace ya nuna misalan rabewar iko tare da inganta damokradiyya a kasar.

Shugaban kungiyar, Alhaji Salisu Magaji, ya bayyana yabon ne jiya (Lahadi) a Bauchi yayin da yake bayyana ra’ayinsa akan jawabin da jagoran jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu yayi, cewa shugabancin Bukola Saraki ta kasance mai gaba da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Har ila yau, Magaji yayi Allah wadai akan jawabin da kungiyar labaran Buhari ta gabatar wanda shugaban ta Niyi Akinsiju da sakatarenta Cassidy Madueke suka sa hannu, wanda ke goyon bayan jawabin Tinubu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel