Sokoto ba tushenka bane – Kungiya ga Atiku

Sokoto ba tushenka bane – Kungiya ga Atiku

Wata kungiyar yan Sokoto mai suna “Concerned Citizens of Sokoto State”, ta nisanta kanta daga ikirarin da dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) Aitiku Abubakar yayi na, cewa mai yiwuwa asalin mahaifinsa daga jihar Sokoto ne.

Yayin da suke jawabi ga manema labarai a jihan, kungiyar, wacce Aminu Bala Sokoto ke jagoranta, yace mutanen karamar hukumar Wurno, jihar Sokoto suna matukar kin Atiku Abubakar.

A cewar shi, tsohon mataimakin shugaban kasar ya nemi wata asalin ba jihar Sokoto ba.

Sokoto ba tushenka bane – Kungiya ga Atiku

Sokoto ba tushenka bane – Kungiya ga Atiku
Source: UGC

Mista Bala, wanda ya kasance jagora mai ritaya a aikin soja, yace: Atiku wanda a halin yanzu ya wuci shekaru 72 bai taba danganta kansa da Wurno ba, hedikwatan karamar hukumar Wurno a jihar Sokoto, inda yake ikirarin cewa daga nan kakansa ya fito.

KU KARANTA KUMA: PDP da fadar Shugaban kasa sun yi musayar kalamai kan tafiyar Buhari Birtaniya

A baya mun ji cewa wani basarake daga masarautar Dutse ta jahar Jigawa ya tabbatar da ikirarin da tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi na cewa mahaifiyarsa yar jahar Jigawa ce, inda bada tabbacin lallai mahaifiyar Atikun diyarsu ce, Atiku kuma jikansu ne.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan basaraken da baya bukatar a bayyana sunansa ko sarautarsa ya bayyana cewa mahaifiyar Atiku diyace ga marigayi Malam Abdullahi dan asalin Jigawar Sarki ta jahar Jigawa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel