APC ta kara samun karfi yayinda Amaechi da Akpabio suka magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu, sunyi alkawarin aiki tare (hoto)

APC ta kara samun karfi yayinda Amaechi da Akpabio suka magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu, sunyi alkawarin aiki tare (hoto)

Manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyu daga yankin kudu-maso-kudu, Hon. Rotimi Chibuike Amaechi da kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio sun magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu.

A cewar wata sanarwa da aka aiko ma Legit.ng daga Festus Keyamo, daraktan sadarwa na kungiyar kamfen din Shugaban kasa na APC, anyi ganawar ne a bangaren Sanata Akpabio.

Jiga-jigan jam’iyyar biyu Alhaji Nasiru Danu, (Dan Amarna na Dutse) da Keyamo ne suka karya gabar a ranar Lahadi, 28 ga watan Afrilu.

APC ta kara samun karfi yayinda Amaechi da Akpabio suka magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu, sunyi alkawarin aiki tare (hoto)

APC ta kara samun karfi yayinda Amaechi da Akpabio suka magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu, sunyi alkawarin aiki tare
Source: UGC

Alhaji Danu ya kasance daya daga cikin daraktocin kungiyar kamfen din Shugaban kasa na APC kuma tsohon dan kashenin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda Keyamo ya kasance jigon jam’iyyar daga yankin kudu maso kudu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rashin hallaran alkali ya tsayar da gurfanar da zababben gwamnan Bauchi

APC ta kara samun karfi yayinda Amaechi da Akpabio suka magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu, sunyi alkawarin aiki tare (hoto)

Amaechi da Akpabio sun magance tsohuwar gabar da ke tsakaninsu
Source: UGC

Taron wanda ya gudana a gidan Danu a yankin Askoro na Abuja ya dauki tsawo awowi da dama inda shugabannin suka tattauna game da sabani daban-daban daga lokacin da suke a matsayin gwamnonin PDP da kuma kungiyar gwamnonin Najeriya a waccan lokacin.

Sun kuma tattauna sannan suka duba kokarin jam’iyyar a yankin kudu-maso-kudu a zaben da aka kamala sannan su ka duba yankunan da abubuwa suka baci da kuma yadda za a inganta su a nan gaba.

Shugabannin biyu sun amince suyi aiki tare domin ci gaban jam’iyyar a kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel